Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta nuna damuwa kan ƙarancin ma’aikatan wucin gadi da take fuskanta domin gudanar da babban zaɓen 2027, tana mai danganta hakan da rahotannin tashin hankalin siyasa a sassan ƙasar, wanda ta ce ya raunana sha’awar masu son neman aikin, musamman mambobin ƙungiyar Yi Wa ƙasa Hidima (NYSC).
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa Daraktar Wayar da Kan Masu Zaɓe da Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Victoria Eta-Mesi, ce ta bayyana hakan a ranar Talata, yayin wata tattaunawa da aka yi da ita a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels.
Ta ce har yanzu INEC ba ta samu adadin masu neman aikin da take buƙata domin fara horas da ma’aikatan da za su gudanar da ayyukan zaɓen ba.
A cewarta, tashe-tashen hankulan siyasa da aka samu a baya-bayan nan a sassan ƙasar sun hana mutane, musamman ’yan bautar ƙasa, neman aikin wucin gadi da za su gudanar yayin zaɓe.
Ta ce, “Ba mu samu adadin mutanen da muke buƙata domin horaswa don zaɓen ba.”
Ta ƙara da cewa, “Muna ƙoƙarin ƙara yawan mutanen da za su shiga aikin zaɓe. Kuma tabbas, hakan ya fara shafar shigar ’yan bautar ƙasa da sauran matasa maza da mata cikin aikin zaɓen.”
Eta-Mesi ta danganta ƙarin wa’adin yin rajistar ma’aikatan wucin gadi da hukumar ta yi a baya-bayan nan da ƙarancin masu neman aikin, wanda ta ce tashin hankalin siyasa da ake samu akai-akai a ƙasar na daga cikin abubuwan da suka haddasa hakan.
Ta bayyana cewa, “Ba mu samu adadin mutanen da muke buƙata domin horaswa don zaɓen ba, shi ya sa ma muka ƙara wa’adin rajistar, saboda ba mu samu adadin da muke buƙata ba. A ƙarshe, hakan ba ya yi wa aikinmu kyau.”
Da take ƙarin bayani kan yawaitar tashin hankalin siyasa, jami’ar INEC ta ce rikice-rikicen da ake samu yayin harkokin siyasa na ƙara wa hukumar wahalar gudanar da ayyukanta, tana mai cewa mafi yawan saƙonnin wayar da kan jama’a da hukumar ke yaɗawa sun fi mayar da hankali ne kan hana tashin hankali.
Ta ce, “Yawancin saƙonnin wayar da kanmu sun fi mayar da hankali kan rashin tashin hankali, saboda tashin hankalin yana ƙara mana wahalar aiki. Muna ƙoƙarin ƙara yawan mutanen da za su shiga aikin zaɓe.”
Domin magance ƙarancin ma’aikata, INEC ta buɗe shafinta na neman ma’aikatan wucin gadi a ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2026, domin ’yan Nijeriya da suka cancanta su yi rajistar shiga aikin zaɓen 2027.
An tsara rufe rajistar ne tun farko a ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026, amma daga bisani hukumar ta ƙara wa’adin da makonni biyu domin bai wa ƙarin mutane masu cancanta damar yin rajista, tare da samar mata da isassun ma’aikatan da za a tura sassan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe (IVEC), Mohamined Kudu Haruna, ya fitar, hukumar ta ce ƙarin wa’adin zai bai wa ’yan Nijeriya masu cancanta damar neman aikin.
Sanarwar ta ce, “An ƙara wa’adin ne domin bai wa ƙarin ’yan Nijeriya masu cancanta damar neman aikin, tare da tabbatar da cewa hukumar ta samu isassun masu neman aikin da za a iya tura su sassan ƙasar.”
Hukumar ta buƙaci ’yan Nijeriya da suka cancanta su yi amfani da ƙarin wa’adin wajen kammala rajistarsu.
Ta ce, “Bayan nazarin yadda aikin rajistar ke gudana, hukumar ta ƙara wa’adin da makonni biyu. Yanzu za a rufe shafin rajistar da ƙarfe 11:59 na dare, ranar Laraba, 3 ga Disamba, 2026. Ana tunatar da masu neman aikin cewa rajista za ta gudana ne kawai ta shafin INECPRES, wanda kuma za a iya shiga ta shafin intanet na hukumar.”
