Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi al’ummar Igbo da ke zaune a Jihar Legas da su zaɓe shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai amincewa cewa ya yi fushi da su saboda rashin zaɓensa a zaɓen 2023.
Tinubu ya yi wannan roƙo ne ranar Litinin yayin wata ganawa da matasa, dattawa da shugabannin al’ummar Igbo a Cibiyar Fasaha ta Wole Soyinka da ke Legas.
Shugaban ya bayyana ’yan kabilar Igbo a matsayin ’yan uwansa, yana mai cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da haɗin kan ƙasa da shugabanci mai bai wa kowa dama.
Ya kuma buƙaci al’ummar da su mallaki katin zaɓensu (PVC), tare da mara masa baya da sauran ’yan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Da yake magana kan zaɓen 2023, Tinubu ya ce ya ji haushi ganin yadda wasu daga cikinsu ba su zaɓe shi ba, amma ya ce yanzu an sasanta.
“Wasu daga cikinku ba su zaɓe ni ba a 2023, na yi fushi. Amma yanzu mun sasanta. Ku mallaki PVC ɗinku, kuma a wannan karon za ku zaɓe ni,” inji shi.
Tinubu ya kuma tabbatar da aniyarsa ta neman wa’adi na biyu, yana mai cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba shi damar sake tsayawa takara.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta sanya ranar 16 ga Janairu, 2027 a matsayin ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya.
A zaɓen 2023, Tinubu ya sha kaye a Jihar Legas, wadda ta kasance babbar cibiyar siyasarsa tun shekarar 1999, inda Peter Obi na jam’iyyar Labour Party ya kayar da shi.
