Alƙawarin tallafin miliyan N100 da Hon. Diso ya yi wa gidauniyar I.S. Linda ya jawo shakku

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Hon. Garba Ibrahim Diso, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar ƙaramar Hukumar Gwale a Majalisar Tarayya da ke Abuja, ya yi alƙawarin tallafa wa Gidauniyar I.S. Linda, mai haɗin gwiwa da ƙungiyar Safinatul Khairi da ke Unguwar Diso cikin birnin Kano, da naira miliyan 100.

Ya ce tallafin zai taimaka wa gidauniyar wajen ci gaba da tallafa wa marayu da sauran marasa ƙarfi, ba su jari da koyar da sana’o’i domin su samu dogaro da kai da taimakon Ubangiji.

Sai dai, a lokacin da aka yi alƙawarin tallafin a wajen taron bayar da jari da kayan sana’a ga mutane sama da 300, wanda Gidauniyar Ibrahim S. Linda Foundation ta gudanar ranar Asabar a Kwalejin Nazarin Shari’a da Harshen Larabci, wato Legal, mahalarta taron ba su nuna farin ciki ko tafi sosai ba.

A al’ada, ana jin mutane na murna ko tafi idan wani ya yi kyauta ko bajinta a taro. Amma wannan karon, bayan ɗan majalisar ya yi alƙawarin bayar da naira miliyan 100, mahalarta taron ba su nuna murna a fili ba sai da mai gabatar da taron ya nemi su tafa. Wasu kaɗan ne suka tafa, yayin da wasu da ke wajen taron ke cewa ba zai cika alƙawarin ba.

Wannan ya nuna cewa jama’a sun nuna shakku kan ko ɗan majalisar zai cika alƙawarin bayar da tallafin, duk da cewa wasu sun bayyana cewa idan aka yi sa’a, zai iya bayar da kuɗin a wannan karon.

Bayan jin maganganu da ra’ayoyin mahalarta taron, ’yan jarida sun yi ƙoƙarin jin ta bakin Hon. Garba Ibrahim ɗiso bayan ya fito daga taron, domin jin abin da zai ce kan shakkun da wasu suka nuna game da alƙawarin tallafin naira miliyan 100.

Sai dai ƙoƙarin ya ci tura, inda ya ce wa ’yan jarida: “Ku yi haƙuri, sai wani lokaci.”

Taron ya samu halartar manyan mutane, malamai, ’yan kasuwa, ’yan siyasa da sauran al’umma, waɗanda da dama suka bayar da gudummawa ga gidauniyar tare da bayyana gamsuwarsu ta hanyar yabawa shugaban Gidauniyar Alhaji Ibrahim S. Linda Foundation.

By ukarofi

Leave a Reply