Aƙalla mutum 15,000 ne suka kamu da Tarin-fuka a Jihar Legas a 2024 – Kwamishina

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamishinan Kiwon Lafiya na Jihar Legas Akin Abayomi ya bayyana cewa an gano mutum 15,000 dake ɗauke da cutar tarin fuka a 2024 a jihar.

Abayomi ya ce alƙaluman yaɗuwar cutar sun nuna cewa akwai yiwuwar mutum 32,000 sun kamu da cutar inda a ciki an gano 15,000 sauran 17,000.

Kungiyar Kiwon Lafiya tana Duniya WHO ta bayyana cewa Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afrikan da cutar ya fi yaɗuwa.

Bincike ya nuna cewa cutar na yin ajalin aƙalla mutum 268 a rana saboda rashin sani, rashin mai da hankali wajen gudanar da bincike domin gano cutar da rashin yi wa mutane gwajin cutar.

Tarin fuka cuta ce da ake iya kamuwa da ita ta iska inda a dalilin tari ko atishawa da wanda ke ɗauke da cutar ya yi mutum na iya kamuwa da cutar.

“Yara ƙanana musamman ‘yan ƙasa da shekara biyar na daga cikin rukunin mutanen da suka fi kamuwa da cutar a dalilin rashin sani, rashin mai da hankali wajen gano cutar da wasu jami’an lafiya ke yi ,rashin asibitin kula da masu fama da cutar musamman a yankin karkara da sauran su.

Uwar gidan gwamnan jihar a wajen taron ta karrama matan shugabanin ƙananan hukumomin jihar.

Uwar gidan gwamnan ta yi kira ga matan da su zage damtse domin gano sauran mutanen da ke ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba a jihar.

By ukarofi