A Daura za a yi jana’izar Buhari, inji Raɗɗa

Spread the love

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa ya ce iyalan Muhammadu Buhari sun yanke shawarar yi masa jana’iza a garin Daura, mahaifarsa dake jihar ta Katsina.

Da ya ke magana da kafar yaɗa labarai ta DW Hausa, Dikko Raɗɗa ya ce yana birnin na Landan ya samu labarin rasuwar inda ya je duba shi.

“Na zo ranar Juma’a domin duba shi, muna shirin dawowa gida kuma sai ga labarin rasuwar tasa,” inji shi.

“Yanzu muka rabu da iyalansa a asibitin da ya rasu kuma an yi ittifaƙi za a kai shi gida Daura a jihar Katsina domin yi masa sutura. Insha Allahu za su baro Ingila da safe.

“Muna sa ran gobe Litinin za a yi jana’izar tasa saboda muna sa ran mataimakin shugaban ƙasa zai iso Ingila cikin dare, su taho da mamacin da safe.”

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima ya je Landan domin raka gawar Buhari zuwa gida Nijeriya.

By Babaji