Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana cewa za a yi jana’izar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a mahaifarsa dake Daura, Jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne yayin da aka tabbatar da rasuwar tsohon shugaban ƙasar a birnin Landan.
Gwamna Raɗɗa, wanda yanzu haka ke ƙasar Ingila, ya tabbatar wa da DW Hausa cewa ana ci gaba da shirye-shirye domin kawo gawar tsohon shugaban ƙasar gida domin gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
