Xabi Alonso zai iya? Ga Amsar

Spread the love


Daga MUTTAKA A. HASSAN

Kamar yadda na faɗa ne a baya, cewa Ancelotti yana da ƙwarewa fiye da Alonso, haka ne ina kan wannan maganar har gobe. Amma sallamar wanda ya fi ƙwarewa a kawo wani na nufin an ci baya? Ba haka ba ne…duka yana cikin gyara. Komai ƙwarewar mutum, lokacinsa na ƙarewa ta yadda za a buƙaci wani ya zo ya gwada tasa basirar, shi ne abin da ya faru.
Amma akwai ci gaba a wasanni biyun farko da Alonso ya buga? Akwai alamar zai iya cin Club World Cup da ake bugawa? Ko da Real Madrid ta doke kowa a wannan kofi, adadin wasannin ba zai isa ya zama hujjar Alonso zai iya ko ba zai iya ba, haka ma idan ba a ci ba.
Wasu na iya tambaya: To, yaushe ne ya dace a fara hukunci kansa? Amsa ba ta da sauƙi. Babu wata ƙa’ida madaidaiciya. Amma abin da za mu iya yarda da shi shi ne: Ba za ka fahimci komai da gaske ba sai lokacin da mafi yawan ‘yan wasa suka dawo daga jinya, da fafatawa da ƙwararrun ƙungiyoyi masu ɗauke da tsari (tactics) da kuma samun akalla wasanni 20 zuwa 25 da mafi yawan ‘yan wasa na sha ɗayan farko a cikin tawaga. A lokacin ne tsarin wasa ke fara bayyana yadda ya dace, yadda ƙungiyar ke kai hari da kare kai cikin daidaitattun alamamomi. A lokacin za ka iya gane ko kocin ya daidaita da salon wasan riƙe ƙwallo (ball possession) ko kuma salon sauya hari cikin sauri (counter attack). Tun lokacin da Alonso ya sauka a Madrid, mutane sun yi ta magana a kan “Sabon tsari/New tactics.” Don haka idan ana maganar sauya tsari, sai an yi haƙuri don yana ɗaukar lokaci.
Halin da Ancelotti ya bar ƙungiyar har yanzu yana nan, kuma wasu ‘yan wasa za su fuskanci ƙalubale wajen sabawa da sabon koci mai ɗauke da ra’ayoyi masu buƙatar ƙoƙari. Kada mu manta cewa kafin wasan Real Madrid da Al-Hilal, Alonso bai yi wa ‘yan wasa atisaye da yawa ba (na farko ma rabin tawagar ne kawai suka halarta saboda wasu suna wakiltar ƙasar su). A gefe guda kuma, sababbin ‘yan wasa har yanzu na isowa. Za su buƙaci lokaci ba don kawai su fahimci tsarin Alonso ba, har ma su fahimci falsafar kulob ɗin, da sabawa da birnin da ma mu’amala da saura.
Mutane ya kamata su tuna: Abin da ke jiran Alonso ba tsarin wasa kawai ba ne; har da sauya halin tunani na wasu ‘yan wasa.
Ga masu ganin cewa Perez ya ɗauki haɗari ba tare da yin lissafi ba wajen ɗaukar Alonso, ni kuwa zan ce akasin haka. Idan akwai lokacin da ya dace a ɗauki mataki mai ƙayatarwa da gwada sabon salo; lallai yanzu ne. Wato lokacin da aka hango matsala tun tana ƙarama kafin ta gawurta ta zama ƙurar da aka ajiye a garken awaki ba takunkumi.
Duk da haka, dole mu yaba da wasu alamomi masu kyau da aka gani a wasanmu da Al-Hilal. Yanzu ƙungiyar na da ɗan baya da ke iya fasa layuka (line breaking passes) da kwallayen sa, tsarin matsa lamba yana fara ƙayatarwa, kuma dabara ta tsare layi a gefen fili ta yi tasiri har zuwa yanzu. Har wa yau, samuwar Gonzalo Garcia da damar da aka ba shi a rashin Mbappe da yadda yaron ya nuna zai iya, alamu ne na ƙwarewa daga Alonso, yadda ya yarda da yaro ƙarami ya fara da shi a wasanni biyu a jere; duka mun sani idan Ancelotti ne ba zai yi la’akari da yaron shi ne lamba 9 na asali (natural CF) a ƙungiyar ba; zai ɗauko wani babban ɗan wasa da ba wurin yake bugawa ba ya saka shi (out of position) wanda hakan na daga abin da ya fara bayar da matsaloli
Har wa yau, a wasa na biyu da aka buga da Pochua, kai-tsaye salon wasan ya yi kyau haka ma sakamakon. Amma ba za a fahimci wani abu kyakkyawa da ya dace a dogara da shi ba saboda dalilai biyu:
1. Mun samu jan kati a mintuna 10 na farko, dole ne salo ya sauya daga yadda coach ya tsara za mu gani.
2. ƙungiyar ba ta iya doke kowace ƙungiya ba a gasar.
ƙwallon ƙafa ba ta da tabbas, abubuwa na iya sauyawa cikin gaggawa. Shi ya sa a wasanni kaɗan ba a iya yanke hukunci, don su fitila ne kawai, ba alama ba. Kada mu yi gaggawar yanke hukunci bisa sakamakon gajerun lokuta; ko da sun zama masu kyau (an ci Club World Cup) ko marasa kyau (an rasa kofin). Mu yarda da tsarin, mu sani gaba ta fi baya yawa. Hala Madrid!

Muttaka A. Hassan, a.k.a Shatan ‘Yan Madari, mai sharhi ne a kafafen zumuntar yanar gizo

By ukarofi