Netanyahu: Jikin ta ƙaura ya yi sanyi

Spread the love

Daga MUBARAK UMAR

Idan ka kalli bidiyon Benjamin Netanyahu a jiya, sai kuma ka koma baya ka kalli wanda ya yi ranar da ya shelanta kai wa ƙasar Iran hari, za ka fahimcu jikin ta ƙaura ya yi sanyi.
Psycho-Analysis of Leaders ilimi ne mai zurfin gaske kan nazarin yadda shugabanni ke sauya hali, zai baka damar gane ina suka dosa, ko da kuwa ba su furta abin da bakinsu ba, abin da kawai ake yi shi ne bibiyar maganganunsu da rubuce-rubucensu.
Mene ne ke haddasa haka?
Tsoron asara: Lokacin da shugaba ya ji haɗarin rasa iko ko goyon bayan jama’a, yana sauya hali don ya jawo tausayi.
Kare Kai (Defence Mechanism): Zuciyarsa na ƙoƙarin kare shi daga jin kunya ko faɗuwa, ta hanyar sauya salo daga mai faɗa zuwa mai neman jin ƙai.
Sigmond Freud ya yi bayani cewa halayyar ɗan adam na ta tafiya bisa “unconscious” – wato tunanin da mutum bai san yana da shi ba. Shugabanni, a daidai lokacin da suke cikin matsin lamba ko suka fuskanci barazana daga jama’a ko abokan gaba, halin da ba su san suna da shi ba — kamar tsoro, kunya, ko rashin tabbas — yana fara bayyana a kalamansu da yanayin jikinsu.
Misali, shugaba na iya fara magana da ƙarfi, izza da faɗa, kamar yadda Freud ke cewa yana amfani da “ego” don kare kansa da matsayinsa. Amma daga baya, lokacin da ‘reality principle’ ya bayyana — wato gaskiyar cewa iko ba ya dawwama ko akwai barazana — sai ya koma amfani da defence mechanisms kamar “projection” (zargi wasu da laifin da shi ne da kansa ya aikata) ko “reaction formation” (fuskantar akasin abin da yake jin tsoro daga gare shi).
Dr. Jerrold Post, malami ne da ya yi fice a nazarin halin shugabanni masu tsaurin ra’ayi, ya bayyana cewa shugabanni masu irin wannan sauyin hali na da “narcissistic personality” – suna jin su na da fifiko, amma suna da tsananin tsoron faɗuwa ko jin kunya. Wannan yana jawo su riƙa sauya magana daga ƙarfi zuwa ƙorafi domin su kare kansu daga illar cikin gida da ta waje.
Psychoanalysis na koyar da mu cewa duk da cewa shugabanni suna da iko, da harshe mai ƙarfi, akwai wani sirrin da ke tattare da tunaninsu wanda ke bayyana a lokacin da iko ya fara ja baya. Wannan yana da amfani wajen tantance ko shugaba yana faɗar gaskiya ko kuwa yana amfani da salon ne don ya tsira daga matsin lamba.
Misali, Adolft Hitler yana ɗaya daga cikin shugabannin da Jerrold Post da Harold Lasswell suka fi nazari a kan ɗabi’unsa. A farkon mulkinsa, Hitler ya kasance mai amfani da kalmomi masu tsauri da nuna karfi, yana cewa: “Za mu kafa sabuwar Jamus da kowa zai ji tsoronmu!”
Amma bayan ya fara fuskantar matsin lamba daga gamayyar sojojin yamma a lokacin yaƙin duniya na biyu, da koma bayan soji, ya koma kiran kansa wanda duniya ta ƙulla masa makirci, yana cewa Yahudawa, Amurka da Tarayyar Soviet suna kokarin rusa Jamus.
Saboda haka idan ka kalli Netanyahu, sai kuma ka yi amfani da “Psychoanalytic Interpretation” za ga gane yadda yake amfani da “rationalisation” da “victimisation” don bayyana kansa da ƙasarsa a matsayin waɗanda ake ƙoƙarin danne su. Yana gujewa fuskantar laifi ko zargi ta hanyar fassara mamayarsa a matsayin kare kai.

*Mubarak ɗan jarida ne a Abuja

By ukarofi