Tuna baya (25 ga maris, 2024): Yadda ɗillin ta kan yi ɗillin

Spread the love

Daga COMRADE IBRAHIM ABDU ZANGO 

Gizo a tatsuniya, wani mutum ne makaryaci wani lokaci kuma mai abin dariya. Haƙiƙa da wuya kaji tatsuniyar Gizo babu sakarci ko gabanta, kuma mai daurewa da sakarcin gizo sai dai matarsa wai ita ƙoƙi. To akwai wata waƙa da gizon yakanyi wato kamar haka: aiyuriri yuriri ga amare  ai tafiya dai ai ban manta ba, a a dara kulle adakulle kudum kudum! Gaskiyar lamari sai yanzu wata tsohuwa take fassara mana ma’anar Hausar Bahaushe, wani Bamagujen Sarki a Dutsen Dala: yadda ta banun labarai sai ya dace da wannan zamani da muke ciki wato tun daga lokacin farar hula har ya zuwa na sojoji, kasan juyin mulkin sojoji yazo Afrika ne ta hannun sojojin Masar wato Alƙahira, sannan ya shigo mana Afrika ta yamma da farko Ghana, wacce akayi wa shugaba Nkurmah, shugaban da yaso ha haɗe kan Afrika kuma akan haka ne akayi amfani da sojoji a Ghana masu kwaɗayin mulki suka aikata abinda ya zama kazanta ga dukkan Afrika tun daga wancan lokaci har ya zuwa yanzu. Kaga dai bayan Ghana sai kuma Nijeriya a shekarar 1966, juyin mulkin da ya haddasa yaƙin basasa wanda har gobe shine ya janyo gaba da durƙushewar cigaban Nijeriya.

Na san dai ƙazamin yanayin yadda aka rungumi adawar siyasa musamman waɗanda basuyi nasarar cin zaɓe ba sune kusan ummul aba’isin kawo ruɗani, su ka kuma bawa sojoji goyon baya, domin canza gwamnati wanda daga ƙarshe aka shiga halin ni ‘yasu, domin kamar yadda marigayi Malam Aminu Kano yace, matuƙar soja ya shigo mulki to abune mai wuya ya bada mulki cikin sauƙi! Kaga dai sai da Janar Gowon ya shekara tara yana mulki bayan yayi alƙawarin zai bayar cikin ƙanƙanin lokaci sai daga baya masu jin daɗin mulkin suka canza masa ra’ayi, wanda daga ƙarshe wasu sojojin suka tunkuɗe shi, wanda cikin ƙanƙanin lokaci suka kawo canje-canje, kususan a shekarar 1967 suka ƙirƙiro ƙananan hukumomi, wanda a yanzu suka tasamma 774, shi kuma shugaban gwamnatin wato marigayi Janar Murtala Ramat Muhammad yayi mulki mai tsafta domin niyyarsa taimakawa talakawa ne, amma ina maƙiya sunyi yadda sukayi suka kashe shi a ranar Juma’a zai tafi masallacin Juma’a da rana ƙiri-ƙiri!

 Gaskiyar lamari mulkin soja yayi rawar gani ganin ƙirƙiro jihohi 36 da kuma ƙananan hukumomi 774, wanda farar hula baza su iya ba, saboda gaskiya ‘yan siyasarmu kususan na 1999 zuwa yanzu bazasu iya taɓuka komai ba, illa surutu barkatai wand aba zai kaimu ko’ina ba, kususan mu talakawa waɗanda mune kashi tamanin da takwas (88%) na yawa, amma baza kaji wani ɗan siyasa yayi tsokaci domin talaka ba, sai kawai mashalo da abin takaicis zancen wasu masu baki ta kunu, leɓe da dartsa, hanci da majina daga basu ‘yan kuɗi ƙalilan sai su shiga Radiyo suna zugashi bayan ba abinda yakamata yayi yakeyi ba, sai dai kwana a hotel idan ya dawo daga yawon Jambori na Abuja, garin ma’abota jari hujja!

Gaskiya ‘yan siyasarmu basa tausayinmu, sai dai ƙalilan daga cikinsu, domin sun shiga tandun zuma sun barmu da kwankwaɗar zaƙami, wanda daga ƙarshe zai kaimu ga halaka! Gaskiyar lamari baza muce komai ba tun lokacin wata aba wai Korona “Corona Virus” wacce ak akulle duniya kafɗinta. E, duniya mana tunda hatta babban wurin ibadarmu na Makka wato Ka’aba saida aka rufeta na tsawon watanni, Allah shi tsare, mun sha wuya lokacin Korona, ban sani ba ko a lokacin gwamnati da muƙarrabanta sun taimakawa jama’a, wannan dai ban sani ba, sai dai nasan wani attajiri wani mai kamfanin BUA ya shiga lungu-lungu a Kano ya bawa jama’a abinci, sukari mai da sauransu. Ana cikin wannan taraddadi sai kuma aka fito da zancen canzawa Naira fasali wanda gwamnati Shugaba Buhari tayi gaskiya an shiga rudu da hayaniya marar kwantatuwa, domin abin akwai kaico ƙwarai da gaske, sai me zamuyi illa addu’a?

Muna cikin wannan kwatsam sai ga kuma sabuwar gwamnati ta kawo wani sabon salo an cire tallafin man fetur wanda take cewa wasu ƙalilan ne ke morarsa, kuma zai bata damar tara kuɗaɗen da wai zata yiwa jama aiki! Allahu Akbar, cire wanan abu sai ya ɗorawa talakawa wani sabon bala’i, domin a yau akwai gidaje fiye da miliyoyi waɗanda basa iya cin abinci koda sau ɗaya, bama sau uku ba, an mayar da mutane da yawa almajirai, yara matasa sun zama ɓarayin waya da haura gidajen bayin Allah, wannan duk sanadin janye tallafi ne, ashe dai tallafin bawai masu kuɗi ya takurawa ba, harda miliyoyin talakawan Nijeriya. Kamata yayi na kusa-kusa da shugaba Tinubu su ankarar dashi cewa talakawan Nijeriya kafɗinsu suna cikin ɗimuwa ta yunwa, kishirwa da shiga hannun masu garkuwa da mutane, haƙƙinsa ne ceto jama’ar Nijeriya kafataninsu domin fita daga masifu iri-iri waɗanda ya gada daga gwamnatin baya wadda jama’a suka zaɓa daga baya ta juya musu baya, Hasbunallahu Wani’imal Wakil. Haƙƙin Tinubu ne ya tabbatar da ceton jama’’ daga ababen dake faruwa loko-loko d akuma lungu-lungu na Nijeriya.

Gwamnoni tunda an zaɓe ku, zancen siyasa ko wani kamfen ya ƙare, naji wasu masu baki da kunu suna cewa wai sun kafa gwamnati saboda haka sai nasu kawai babu kowa sai su, kaji jahilci. To sauran miliyoyin mutane korarsu kenan za’ayi, su zama ‘yan gudun hijira kenan? Siyasar shirme kenan daga masu hanci da tasono, waɗanda iblis ya sasu ciki aljihunsa, domin sun fita daga cikin mutanen kirki sai alfasha da nuna mutane da leve!

Naku Comrade Ibrahim Abdu Zango, Chairman: Kano Unity Forum, Kano – Nigeria, 08175472298

By ukarofi