Tare da SHAMSIYYA MANGA
Ko kun san cewar Zubar jini bayan haihuwa na ɗaya daga cikin abubuwan da suke saurin janyo mace-macen mata bayan haihuwa.
Shin mene ne zubar jini bayan Haihuwa?
Postpartum Haemorrhage (PPH)
Zubar jini bayan haihuwa: Jini ne da yake zuba sosai cikin awanni ashirin da huɗu bayan mace ta haihu, wanda zai iya kai wa adadin sama da lita ɗari biyar (500ml).
Ire-iren Zubar jini bayan haihuwa.
Zubar jini bayan haihuwa ya kasu kashi biyu . Akwai.
1. Primary Postpartum Haemorrhage
2. Secondary Postpartum Haemorrhage.
Shi na farko watau Primary PPH:
Shi ne zubar jini a cikin awanni ashirin da huɗu na haihuwa.
Shi kuma Secondary PPH:
Shi ne zubar jini bayan haihuwa a cikin awanni arba’in da takwas ko sama da haka na haihuwa.
Mene ne abubuwan da suke janyo zubar jini bayan haihuwa?
Abubuwan da suke janyo zubar jini bayan haihuwa a turance ko na ce a likitance ana kiransu da 4T’s. Watau T guda huɗu.
1. Uterine Atony (Tone)
2. Tissues
3. Trauma
4. Thrombin.
1. Shi na farko shi ne rashin kamowar mahaifa yadda take. Watau (Inability of the uterus to contract).
2. Shi kuma na biyu shi ne a samu sauran mabiyiya ko wani sauran dattin jinin haihuwa a mahaifa.
3. Shi kuma na uku shi ne a samu yagewar wasu daga cikin fatacocin gaban mace ko cikin mahaifa.
4. Na huɗu kuma idan mace tana da wata matsala ta zubar jini.
Alamomin da za a gane mace ta samu zubar jini bayan haihuwa.
1. Zubar jini sosai wanda har za a iya ɓata audugar mata sama da ɗaya ko biyu a cikin awa guda.
2. Bugun zuciyar mace zai ƙaru a kai a kai.
3. Jininta zai yi ƙasa(Blood pressure).
4. Jikinta zai yi fari.
5. Za ta dinga jin hajijiya.
6. Za ta dinga ganin duhu-duhu.
Yadda za a magance shi.
1. Za a sanyawa mace ƙarin ruwa (IV Fluid) yawanci Normal Saline domin a taimaka wajen daidaita Sauƙar jinin nata (Low blood pressure).
2. A cikin ruwan za a sanya allurar Oɗytocin guda biyu ko sama da haka a cikin kowane lita ɗaya na ruwan.
3. Za a dinga matsa ƙasan marar mace a hankali domin a taimaka wajen mahaifa ta yi contracting.
4. Idan da buƙatar ƙarin jini a yi gaggawar yi.
Yadda za a kare kai daga samun zubar jini bayan haihuwa.
1. A guji haihuwa a gida.
2. A tabbatar da an duba an ga mace ta samu yaguwa a gabanta ko a’a.
3. A kula wajen cire mabiyiya da fitar da gudajin jini bayan an haihu.
4. A tabbatar an yi allurar Oxytocin bayan an haihu.
5. Idan an cire mabiyiya a duba ta da kyau domin a tabbatar da babu sauran ta da ya rage a mahaifa.
Abubuwan da zubar jini bayan haihuwa yake janyowa.
1. Ƙarancin jini (Postpartum Anaemia)
2. Shock, ko mu ce ƙarancin ruwa da iska a jikin mutum wanda har yake cire mutum a hayyacinsa.
3. Mutuwa idan har ba a ɗauki kulawa ta musamman ba.
©️Shamsiyya Usman Manga (Registered Midwife)
