Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa za a yi duk mai yiwuwa, domin bunƙasa harkar noma da kuma samar da abinci a Nijeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da shugaban Brazil Inacio Lula Da Silva, a daidai lokacin da ake fara taron ƙungiyar ƙasashe ta Brics karo na 17.
A cewar sanarwar da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya ce, wasu tsare-tsare marasa kyau a baya sun taimaka wajen hana samun ci gaba a ɓangaren noma a ƙasar.
Shugaban ƙasar ya faɗa wa takwaransa na Brazil cewa tuni Nijeriya ta fara aiwatar da wasu manufofi domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar wanda zai yi gogayya da sauran duniya, musamman a ɓangaren noma.
Ya ƙara da cewa, a shirye Nijeriya take wajen kulla hulɗa da Brazil don ganin an ɗauki mataki nan take wajen ƙara bunƙasa samar da abinci.
“Za mu aiwatar da duk yarjejeniya da muka amince da Brazil, domin kawo gyara a ɓangaren kasuwanci, sufurin jiragen sama, makamashi, samar da abinci da kuma haƙar ma’adinai,” inji Tinubu.
Ya kuma ce gwamnatinsa na ƙoƙari don bunƙasa harkar kiwon dabbobi.
A nasa ɓangare, shugaba Lula ya tabbatar da cewa za a aiwatar da duk wata yarjejeniya da aka cimma da Nijeriya ba tare da ɓata lokaci ba, don ganin kyautatuwar tattalin arziki da kuma hulɗa tsakanin ƙasashen biyu.
Ministan raya dabbobi Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana bangarori uku na haɗin gwiwa da ƙasar Brazil, da suka haɗa da kula da lafiya da cututtuka, da ayyukan tsafta, da bincike kan kayayyakin ƙwayoyin halitta da sabbin nau’o’in iri.
Gwamnonin jihar Benuwai, Hyacinth Alia; Jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun; Jihar Neja, Mohammed Umar Bago; Jihar Delta, Sheriff Oborevwori; da kuma jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, sun halarci taron ƙasashen biyu.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya bayyana cewa ƙananan hukumomin za su goyi bayan tsarin gwamnatin tarayya na sake fasalin fannin noma.
Abiodun ya bayyana cewa, shawarar da shugabannin biyu suka yanke na hada da taron kasuwanci a yayin ziyarar da Shugaba Tinubu zai kai ƙasar, zai haifar da sabbin dabaru da albarkatu, wanda zai ba da damar samun sakamako mai sauri wajen sauya fasalin noma a Nijeriya.
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, da Darakta Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta ƙasa (NIA), Mohammed Mohammed, sun halarci taron na ƙasashen biyu.
