Gwamnatin Tarayya ta ci tarar DSTv miliyan N766

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar da ke Kare Bayanai ta Nijeriya (NDPC) ta ci tarar kamfanin Multichoice zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan 766,242,500 saboda karya dokar kare bayanan Nijeriya.

Hukumar NDPC ta yi fatali da tarar da aka ci kamfanin gidan Talabijin ɗin mallakin ƙasar Afirka ta Kudu a kwanakin baya bayan ta gudanar da bincike na tsawon shekara guda.

“Binciken wanda ya fara a tsakiyar shekarar 2024 ya samo asali ne sakamakon zargin keta haƙƙin sirri na masu biyan kuɗi na Multichoice da musayar bayanan sirri na ‘yan Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar ta kuma gano cewa Multichoice na aiwatarwa tare da miƙa bayanan sirri da suka shafi bayanan ’yan Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce: “Tsarin sarrafa bayanan da Multichoice ke yi ba shi da tushe, rashin adalci, ba dole ba ne kuma ba daidai ba ne. Wannan babban cin zarafi ne ga haƙƙin sirri kamar yadda yake a sashe na 37 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999.

“Nijeriya na da haƙƙin kare ‘yan ƙasarta, da kuma ikon mallakar bayanai a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa – saboda waɗannan suna da tasiri mai yawa ga bin doka, tsaron ƙasa da ci gaban tattalin arziki.”

Dangane da tsarin gyaran da ta dace, Hukumar ta ce ta umarci Multichoice da ta aiwatar da matakan da suka dace.

Sai dai hukumar ta ce ta gano matakan da Multichoice ya ɗauka kan wannan batu bai gamsar da ita ba.

“Don neman haɗin kai, Hukumar ta umarci Multichoice da ya biya tarar N766,242,500 saboda karya dokar kare bayanan Nijeriya,” inji sanarwar.

Dangane da abubuwan da suka gabata, Kwamishinan NDPC na ƙasa, Dekta Vincent Olatunji, ya ba da umarnin a binciki duk wata kafar da Multichoice ke tattara bayanan ‘yan Nujeriya ta hanyar da ba su bi ba.

Ya ce duk wata kafar da ta aiwatar da bayanan sirri da ta saɓa wa dokar NDP, to tana da hukunci a ƙarƙashin dokar.

By ukarofi