Katsina akwai ƙorafi – Mustapha Inuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Nijeriya kowa yana ji a jikin Shi, Katsina akwai ‘ƙorafi, Shi ne sabon taken jamm’iyar haɗaka ta ADC a Jihar Katsina a cewar jagoran adawa Mustapha Inuwa.

Mustapha Inuwa ya bayyana haka, a ɗakin taro na continental events centre dake cikin birnin Katsina. A lokacin da ake bikin gangamin jamm’iyar haɗaka ta ADC, tare da bada katin shedar zama cikaken ɗan jamm’iyar ga wasu daga cikin yayan jamm’iyar na jihar Katsina da kewaye.

Ya ci gaba da cewa” mun taru domin kafa tarihi da neman yanci da kuma samun nasara, a cikin wannan tafiya ta ADC,”. Jagoran ya ƙara da cewa” kowa yasan halin da ake ciki, sobada haka daga yanzu kirarinmu idan ance Nijeriya sai muce kowa yaji a jikin Shi, Katsina akwai ƙorafi. Saboda haka idan kowa yasan haka, ina mafita, sai a haɗa kai mu tashi tsaye domin samun shugabanni nagari, ba shugabanni masu zuciyar firauna ba, kuma ba masu halin ɓera ba.

Shugaban jam’iyar ta ADC a jihar Alhaji Usman Musa a nasa jawabin kira yayi ga ya’yan jam’iyar ya nuna farin cikin sa ne ga yadda al’ummar jihar suka yi tururuwa zuwa cikin jam’iyar a jihar.

Sai yayi kira a gare su da su koma ƙananan hukumomin su domin yi rajista da faɗakar da al’ummar su mahimmancin yin rajista.

“Ta hanyar rajista ne kawai za ku kori zalunci,”inji shugaban jam’iyar.

By ukarofi