Mu na nan daram a PDP – Fatima Garin-Lamiɗo

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu

A daidai lokacin da ake yaɗa jita-jitar wasu yan jam’iyyar PDP sun sauya sheka daga PDP zuwa haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC a jihar Yobe, matashiyar yar siyasa a jihar, Fatima Mohammed Umar (Fatima Garin-Lamido), shugabar ƙungiyar ‘Matasan Inuwar Lema’ a Yobe ta Arewa, ta jaddda goyon bayanta da na jama’arta ga shugabancin Amb. Umar Iliya Damagum da jam’iyyar PDP.

Fatima, dake ƙaramar hukumar Bade a Jihar Yobe, ta bayyana hakan a tattaunawar da tayi da manema labarai, bayan kammala gangami tare da wayar da kan matasa da mata bisa damar da shugabancin jam’iyyar PDP a ƙarƙashin Amb. Damagum ya basu, saɓanin baya inda ba a kula da wahalhalun da mata da matasa suka sha ba wajen bayar da tasu gudummawa.

Ta ce, sakamakon wannan damar ce, PDP ta samu ci gaba a ƙarƙashin sa ta hanyar haɗa kan yayan jam’iyyar ba tare da mayar da mata da matasa saniyar ware ba a kowane mataki a ƙasar nan.

“Bisa ga wannan kyakkyawar manufa ta maigidanmu, Amb. Damagum, mu na kira ga matasa da mata a ƙasar nan, cewa su ci gaba da bai wa PDP cikakken goyon baya da haɗin kai don samun nasara a zaɓen 2027 mai zuwa.”

“Mu a matsayin mu na mata kuma matasa, jam’iyyar PDP ta yi mana goma ta arziki, saboda haka za mu fita lungu da saƙo tare da jan ɗamara domin ganin mun samu gagarumar nasara a zaɓe mai zuwa fiye da wadda muka samu a 2023. Kuma da yardar Allah za mu yi haƙarmu za ta cimma ruwa.

“Bugu da ƙari, a baya ma kowa ya san masu yi mana zagon ƙasa a jam’iyyance, masu ƙoƙarin rarraba kawunan magoya bayan PDP a Yobe, yanzu za a iya cewa anyi walƙiya kowa ya gansu, kuma irin waɗannan mutanen; ko su tafi ko su ci gaba da zama, lokaci yayi wanda ƙarfin PDP zai dawo tare da aiwatar da kyawawan manufofinta ga yan Nijeriya”

A hannu guda kuma, Hajiya Fatima ta yi kira ga matasa da mata a Jihar Yobe da Nijeriya baki ɗaya cewa, su fahimci halin da Nigeria take ciki, su zaɓi jam’iyyar PDP domin sake dawo da sauƙin rayuwa, ta la’akari da mulkin da ta gudanar a lokutan Shugaban ƙasa Obasanjo da Jonathan.

Ta ƙara da cewa, “sannan muhimmin saƙona ga yan Nijeriya, ya kamata mu tuna halascin da PDP tayi mana a baya wajen gudanar da mulkin adalci, inganta al’ammuran tsaro da rayuwar talaka, saɓanin halin da ake ciki yanzu na rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki.”

“Ta ɓangaren ya’yan jam’iyyar PDP, ya kamata mu gane inda gizo yake saƙa, a matakin jihar Yobe da ƙasa baki ɗaya. Saboda ko makaho ya shafa, ya lalaba, ya san tsarin shugabancin Amb. Umar Iliya Damagum a PDP ya kawo muhimman sauye-sauye masu ma’ana, waɗanda za su haɗa kan yayan jam’iyyar PDP, sannan ya bai wa kowa dama ya furta albarkacin bakinsa a dimokuraɗiyyance.

“Sannan abin alfahari ne garemu al’ummar Jihar Yobe, wanda PDP tayi mana alfarma, inda ta amince da miƙa shugabancin jam’iyyar ga babanmu, Amb. Umar Iliya Damagum, wannan abu ne wanda ya dace mu bai wa maras ɗa kunya; mu bashi cikakken goyon bayan don ganin ya kai PDP tudun mun tsira.” Ta nanata.

Fatima Garin-Lamido ta ce ita da tawagarta sun sha alwashin ci gaba da shiga lungu da saƙo wajen wayar da kan mata da matasan jihar Yobe, don samun haɗin kai tare da marawa jam’iyyar PDP baya a kowane mataki, a ƙoƙarinsa na ganin jam’iyyar ta kai ga nasara a zaɓen 2027 mai zuwa.

By ukarofi