Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
A yayin taron jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan gyaran kundin tsarin mulkin Nijeriya, gwamnatin Jihar Kano ta gabatar da buƙatar da ta ja hankalin jama’a: a ƙirƙiri sabuwar jiha daga cikin jihar Kano.
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya wakilta a wajen taron da aka gudanar a Kaduna, ya bayyana cewa wannan buƙata ta zama dole domin sauƙaƙa gudanar da mulki, la’akari da yawan jama’a da girman Kano.
Ƙara kusantar da gwamnati da al’umma, domin inganta walwala da cigaba a yankunan da ke buƙatar kulawa ta musamman.
Ƙarfafa wakilci da cigaba mai ɗorewa, a tsarin mulkin dimokuraɗiyya.
Gwamnatin ta ce ƙirƙirar sabuwar jiha daga cikin Kano ba wai rage mata daraja ba ce, illa kuwa ƙara ma ci gaban al’umma ne.
Wannan na daga cikin sauye-sauyen da ta ce tana fatan za a yi la’akari da su yayin gyaran kundin tsarin mulki.
