Daga USMAN KAROFI a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni a ranar Lahadi cewa a yi ƙasa da tutar Nijeriya a faɗin ƙasar don girmama tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a Landan da misalin ƙarfe 4:30 na yamma bayan fama da doguwar rashin lafiya. Wannan umarni ya nuna alhini da juyayin gwamnati kan rashin tsohon shugaban ƙasa wanda ya shugabanci Najeriya a lokuta biyu a matsayin shugaban soja daga 1984 zuwa 1985 da kuma a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa daga 2015 zuwa 2023.
Shugaba Tinubu ya kuma kira matar marigayin, Hajiya Aisha Buhari, inda ya miƙa ta’aziyyarsa tare da nuna jimami ga iyalan da sauran ‘yan Najeriya. Baya ga hakan, ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima, da ya tafi ƙasar Birtaniya domin rako gawar marigayin Buhari zuwa gida Najeriya don gudanar da jana’iza.
Marigayi Buhari ya kasance ɗaya daga cikin fitattun shugabanni a tarihin Najeriya, wanda aka fi tunawa da ƙwazon sa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma ƙoƙarinsa na inganta tsaro da tattalin arzikin ƙasa. Rasuwarsa ta bar giɓi mai girma a zukatan ‘yan Najeriya da dama, musamman masu kallon sa a matsayin gwarzon gaskiya da rikon amana.
