
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya sanar da rasuwar magabacinsa a mulki, Shugaba Muhammadu Buhari.
Tsohon shugaban ƙasar ya rasu ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 4:30 na yamma bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.
Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga a wata sanarwa da ya fitar a ranar, ya ce Shugaba Tinubu ya yi waya da Aisha Buhari tare da yi mata ta’aziyyar rasuwar mijin nata.
Haka kuma, Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima da ya je Ingila domin ɗauko gawar tsohon shugaban ƙasar zuwa gida Nijeriya.
Sau biyu ana zaɓar Buhari a matsayin Shugaban Ƙasa a 2015 da kuma 2019.
Sannan ya taɓa zama Shugaban Kasa na mulkin soji daga watan Janairun 1984 zuwa Agustan 1985.
Kazalika, Tinubu ya umarci a yi ƙasa da tutoci cikin salo na musamman domin girmamawa ga tsohon shugaban ƙasar.
