A karon farko, Akpabio ya magantu kan zargin cin zarafin Natasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya musanta batun zargin cin zarafi da Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi akansa.

Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, a yayin zaman majalisar bayan hutun mako guda, inda ya ce bai taɓa cin zarafin kowacce mace ba.

Ya ce, shi mutum ne da mace ta raina, don haka yana matuƙar girmama mata, kuma hakan ya sa aka taɓa ba shi kyautar gwamnan da ya fi kowane gwamna iya kula da buƙatun jinsi a Nijeriya.

Ya shelanta cewa, bai taɓa yunƙurin aikata alfasha da Sanata Natasha ko kuma kowacce mace ba a tarihinsa.

Shugaban majalisar ya ƙara da cewa, da shi da ƴan’uwansa mata ne suka girma a hannun mahaifiyarsu, wadda ta rasu a shekarar 2000 a hali na ƙuncin rayuwa.

By Babaji