A rana irin ta yau Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero ya rasu

Spread the love

A rana mai kamar ta yau 23 ga Disambar 1953 ne Sarkin Kano, Alhaji Abdullahi Bayero ya rasu, wanda shi ne na uku da Turawa suka naɗa Sarauta inda ya yi mulkin Kano na tsawon shekaru 27.

Kamar yadda tarihi ya bayyana, shi ne Ciroman Kano na farko da ya zama Sarki kuma na farko cikin sarakuna da ya fara zuwa aikin Hajji, wanda ta dalilin haka ne ma ake kiransa da ‘Sarki Alhaji’.

Bugu da ƙari, a zamaninsa ne aka gina Kwalejin Rumfa (Rumfa College), wadda a lokacin ake kiranta da Makarantar Midil ‘Middle School’.

Har’ilayau, masana tarihi sun tabbatar da cewa, a lokacin mulkinsa ya samar da ci-gaba daban-daban waɗanda suka taimaka wajen bunƙasa Kano.

Me kuka sani ko son sani game da tarihin rayuwar Sarki Alhaji Abdullahi Bayero?

Muna dakon ra’ayoyinku ta wannan lambar: +2347035131313

                *Taskar Nasaba*
          *(Al'adunmu Gadonmu)*
     *Www.taskarnasaba.com.ng*
By Babaji