Fadar shugaban ƙasa ta kira zargin da shugaban Ƙungiyar ƙwadago (NLC), Joe Ajaero, ya yi game da shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan ya yi wa ƙungiyar zamba ta hanyar ƙara farashin fetur bayan sun yi yarjejeniya da ƙungiyar, a matsayin siyasa ce kawai.
Ajaero ya yi zargin cewa ƙungiyar sun yarda da mafi ƙarancin albashi na ƙasa na N70,000 bisa ga fahimtar cewa ba za a ƙara farashin fetur ba.
Sai dai kuma, amsa zargin Ajaero, Babban mai ba Shugaban Ƙasa shawara a Kafafen yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz, a shafin sa na X, @Abdulfagge, ya ce ya halarci taron biyu na ƙarshe inda Shugaba Tinubu ya haɗu da shugabannin ƙwadago, inda ya lura babu inda aka yi irin wannan yarjejeniyar.
Abdulaziz ya bayyana cewa shi kansa ya halarci taron biyu kuma ba a yi wani tayi na cewa ba za a ƙara farashin fetur ba.
“Na zauna a taron biyu da shugaba @officialABAT ya yi da shugabannin ƙwadago kan mafi ƙarancin albashi. A cikin su babu ɗaya daga cikin taron da a ka yi batun ƙarin farashin fetur.
