A yi dokar da za ta hana ‘yan siyasa sauya sheƙa daga jam’iyyar da aka zaɓe su – Dankaka Bebeji

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Gyaran tsarin mulki da shigar da sabbin dokoki abu ne mai kyau da ya kamata a riƙa yi lokaci lokaci saboda abubuwa na canzawa daga wani ƙarni zuwa wani.

Hon. Dankaka Husaini Bebeji jigo a jam’iyyar NNPP mai bai wa Gwamnan Jihar Kano shawara a ofishin mataimakin Gwamna ne ya bayyana hakan.

Ya ce abinda aka yi a baya watakila ba zai yiwu ba a yanzu ya kamata a ce ana samun lokaci ana sake tattaunawa a sake duba irin dokokin da suka daɗe da ba su yi daidai da  zamani ba a sauya su yadda za su amfani al’umma.

Hon ɗankaka Husaini Bebeji ya ce yana goyon bayan matsayin gwamnatin jihar Kano kan neman ƙarin ƙananan hukumomi da jiha 100 bisa 100 domin Kano an yi yawa kuma ba ta samun adalci da ya dace a tsarin rabon albarkatun ƙasa.

Ya yi nuni da cewa domin yanzu akwai jihohin da suka fi Kano samun kuɗaɗe na Gwamnatin Tarayya da ba su kai girmanta ba. Idan kuwa za a samu ƙirƙiro ƙarin jiha daga cikinta za a sami cigaba.

Hon. ɗankaka Husaini Bebeji ya ce shi yana da ra’ayin a yi doka a tsarin mulkin ƙasa ma,  da ya shafi ‘yan siyasa, a yi gyaran tsarin mulki a hana ‘yan siyasa sauya jam’iyya  da aka zaɓe su a ciki   har sai sun gama wa’adin su.

Ya ce domin bai dace a zo a zaɓi wani a jam’iyya A ko B  ko C ba, sannan kuma ya yi tashin gwauron zaɓi ya koma wata, wannan yana koyawa ainihin mambobi da aka zaɓa musamman Musulmi cin amana shi kuma cin amana abu ne mara kyau, duk abinda akace an zaɓe ka a wata jam’iyya  ya zama  komai rigimar da take ciki dole ka haƙura a haka har ka gama.

Hon. ɗankaka Husaini Bebeji ya ce idan da dama ka gama zaka sake shiga zaɓe ka shiga a jam’iyyar in babu dama wasu Allah ya kawo shi kenan, don sha’anin ba nasa ba ne shi kaɗai na al’umma ne domin Allah da ya halicci kowa ya ba shi abinda zai yi iya rayuwarsa.

By ukarofi