Abba Kabir ya gabatar wa Kotun Ma’aikata bayanin kadarorinsa da bashin ake bin sa

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano mai jiran gado, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kadarorinsa da kuma kuɗaɗen da ake bin sa ga Kotun Ma’aikata (CCB) ranar Juma’a a Kano

Abba gida-gida wanda ya samu tarba daga Daraktar CCB ta jihar, Hajia Hadiza Larai Ibrahim, ta ce yadda ya bayyana kadarorinsa na nuna gaskiya da riƙon amana da zai zama ginshiƙin gwamnati mai zuwa a jihar Kano.

“A yau, na cika haƙƙin da tsarin mulki ya ɗora min na bayyana kadarorina kafin in shiga ofis a ranar Litinin 29 ga Mayu,” in ji Kabir Yusuf.

Zaɓaɓɓen Gwamnan, ya shaida wa mai masaukin baƙi cewa aikin gwamnati kira ne kuma hidima ce ga al’ummar Jihar Kano, kuma a shirye yake a koyaushe ya hidimta masu bayan samun amincewarsu.

Haka kuma, Gwamnan mai jiran gado ya bayyana cewa a yanzu haka bakin tekun ya fito don tafiya ta maido da cigaba mai ɗorewa a dukkanin ɓangarori.

Ya kuma ƙara bada tabbacin cewa dukkan jami’an gwamnati da suka haɗa da ma su riƙe da muƙaman siyasa da za su yi aiki a gwamnatin sa za a ba su izinin bin tsarin bayyana kadarorinsu kamar yadda doka ta tanada.

Wannan sanarwar na fitowa ne daga hannun Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan mai jiran gado, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ɗauke da sa hannunsa wadda kuma aka raba wa manema labarai.