Gwamna Buni ya rusa majalisar zartaswarsa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya rushe majalisar zartaswar jihar tare da dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar a ranar Juma’a.

A cikin wata sanarwar manema labaru mai ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun Gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed, inda ya ƙara da cewa an umurci Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) ya miƙa ragamar gudanar da ofishin sa ga Sakataren Din-din-din na fannin mulki.

Haka shi ma Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin jihar, an umarce shi da ya miƙa tafiyar da harkokin ofishin ga Babban jami’in gidan gwamnatin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, sakatarorin din-din-din a ma’aikatu daban-daban a jihar, an umurce su da su karɓi ikon gudanarwar ma’aikatun da suke aiki.

A hannu guda, tsohon Sakataren Gwamnatin jihar, wanda shi ne shugaban kwamitin rantsar da Gwamnan jihar, tare da mambobin sa za su ci gaba da aikinsu, har zuwa ranar da Gwamna ya kammala rantsuwar tare da mataimakinsa.

Gwamna Buni ya yaba wa ‘yan majalisar zartaswar haɗi da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar bisa gagarumar gudumawa da suka bai wa jihar wajen samun nasarorin da gwamnatinsa ta cimma cikin shekaru huɗun da suka gabata.

Haka zalika, Gwamna Buni ya yi musu fatan alheri dangane da abubuwan da suka sanya gaba.