Gwamnati ta ayyana Litinin hutun gama-gari

Gwamnantin Tarayya ta ayyana Litinin, 29 ga Mayu a matsayin ranar hutun gama-gari ga ɗaukacin ma’aikata a faɗin ƙasa.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya bayyana haka a madadin gwamnatin ranar Juma’a a Abuja.

Babban Sakataren Ma’aikatar, Dokta Shuiab Belgore, ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa ‘yan Nijeriya damar shagalin bikin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya na 16.

Sakataren ya ce, “Ministan na taya ‘yan Nijeriya murnar wannan al’amari mai muhimmnci, tare da yaba musu game da tsayin dakan da suka yi wajen zaɓen da ya bai wa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima nasara.”

Ministan ya ce, kasancewar demokuraɗiyya hanyar samar da shugabanci nagari, don haka ya ce ya zama wajibi jama’a su kiyaye dokokkin tsarin domin mara wa gwamnati baya wajen yi wa ƙasa da al’umma hidima yadda ya kamata.

Ogbeni Aregbesola ya kuma yi kira ga ‘yan ƙasa da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da son juna wanda a cewarsa ba a samun nagartacciyar demokraɗiyyar sai da hakan.