Abba Kyari zai koma gidan kaso

A yau wata babbar kotu da ke Abuja ta hana Mataimakin kwamisshinan yan sanda wanda aka dakatar Abba Kyari sabon beli. Saboda haka, zai koma gidan kaso na Kuje.

Mai sharia Emeka Nwite lokacin da yake yanke hukuncin yace, bada belin wani abu ne da kotu in ta ga dama zata bayar ko akasin haka. Ya ƙara da cewa wanda ake ƙarar bai bada wani ƙwakwaran hujja da zai sanya kotu ta sake bada belin nashi.

A 22 ga watan Mayu da ya wuce, kotun ta bada belin Abba Kyari domin bashi damar halartar janaizar mahaifiyar sa. Bayan wannan lokacin ya nemi alfarmar a ƙara masa sati ɗaya wanda kotun ta ƙara masa.

Sai dai a wannan karon, mai shari’a ya hana Abba kyari sabon belin, don haka dole yanzu ya koma gidan kaso na Kuje.