* Sun zargi ma’aikaciyar bankin da zamba
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An samu tashin hankali a birnin Jos ranar Litinin, yayin da wasu gungun kwastomomin Jaiz Bank da suka fusata suka gudanar da zanga-zanga a babban reshen bankin, bisa zargin yin wasu mu’amaloli na damfara da suka jawo asarar miliyoyin Naira.
Masu zanga-zangar, waɗanda ke ɗauke da alluna masu ɗauke da saƙonni, sun yi kira ga Babban Bankin Nijeriya (CBN), ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA) da Gwamnatin Tarayya da su shiga tsakani domin taimaka musu wajen dawo da kuɗaɗensu.
ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, Mista Hashim Faruk, mazaunin ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Plateau, ya yi zargin cewa ya yi asarar Naira miliyan 65 da ya zuba a wani tsarin zuba jari da ake kira Mudarabah a reshen bankin da ke Jos.
Mudarabah wani tsarin zuba jari ne da kwastomomi ke ajiye kuɗaɗensu a banki domin a yi amfani da su wajen gudanar da harkokin zuba jari, sannan su samu riba a ƙarshen wa’adin da aka amince da shi.
Faruk ya ce rikicin ya samo asali ne tun a shekarar 2022, lokacin da wasu kwastomomi suka yi zargin rasa kuɗaɗensu sakamakon wasu mu’amaloli da suka shafi wata ma’aikaciyar bankin.
Ya ce bankin ya kai rahoton lamarin ga Sashen Binciken Laifuffuka (CID) na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Plateau, inda binciken da aka gudanar ya gano wata ma’aikaciyar bankin mai suna Habiba Abdulrahman a matsayin wadda ake zargi da aikata laifin. A cewarsa, ’yan sanda sun ba da shawarar cewa bankin ya mayar wa kwastomomin da abin ya shafa kuɗaɗensu, amma har yanzu bai yi hakan ba.
Da yake magana da jaridar Daily Trust, Faruk ya ce ya zuba Naira miliyan 65 a asusun zuba jarin da ya buɗe da sunansa, da na mahaifiyarsa, matarsa da ’ya’yansa, inda ya riƙa ƙara kuɗi a hankali domin samun riba mai yawa.
Ya ce: “Na ci gaba da ƙara kuɗi a asusuna na Jaiz Bank domin samun ingantaccen jarin zuba jari har zuwa shekarar 2025, lokacin da bankin ya yi alƙawarin ƙara ribar da muke samu bayan ya inganta tsarin aikinsa. Hakan ya sa na ƙara kuɗin da na zuba daga Naira miliyan 50 zuwa Naira miliyan 65 a dukkan asusun zuba jarin.”
Ya ce bayan gano Habiba, an kama ta, kuma an samu nasarar kwato wasu kuɗaɗe ta hannun CID, amma har yanzu ba a mayar masa da nasa kuɗaɗen ba.
Ya yi kira ga hukumomin tsaro da masu yaƙi da cin hanci da rashawa da su shiga tsakani, yana mai cewa yana fama da matsalar ciyar da iyalinsa, biyan kuɗin makarantar ’ya’yansa da kuma sayen magunguna ga mahaifiyarsa da yaransa.
Sauran kwastomomin da suka halarci zanga-zangar sun yi zargin cewa an cire kuɗi daga asusunsu ba tare da izininsu ba. Yayin da wasu suka ce sun zuba kuɗaɗensu a tsarin Mudarabah, wasu kuma sun bayyana cewa kawai sun ajiye kuɗi ne a bankin ba tare da shiga wani tsarin zuba jari ba.
Sun ce a lokacin da suka kai ƙorafi, an sanar da su cewa wata ma’aikaciyar bankin ce ta tura kuɗaɗensu zuwa wasu asusu daban-daban.
Kwastomomin sun dage cewa an gudanar da mu’amalolin ne a cikin harabar bankin, ta hanyar amfani da takardun da bankin ya amince da su.
Wata kwastoma da abin ya shafa, Misis Rose Dayo, ta ce ta buɗe asusun ajiya na ƙayyadadden lokaci (Fiɗed Deposit), inda aka ba ta takardar shaidar ajiya, amma daga baya ta gano cewa an kwashe duk kuɗin da ke cikin asusun.
Ta ce: “Na shiga bankin, na haɗu da wata mata da ban sani ba, wadda ta ba ni fom na cike. Na kammala dukkan komai ta hannun bankin, kuma komai ya tafi yadda ya kamata. Sai da na je cire wasu kuɗaɗe ne bankin ya sanar da ni cewa babu ko sisi a cikin asusun.”
Wata mai zanga-zangar, Zainab Mahmud Dalladi, ta ce an cire kuɗin da ta ajiye domin wani maraya a cikin asusun mijinta ba tare da izininsu ba.
Ta ce: “Shugabannin bankin sun gaya min cewa wata Habiba da ta yi aiki a bankin ce ta cire kuɗin.”
Mu’amalolin sun gudana ne da tsohuwar ma’aikaciya, ba da bankin ba — Jaiz Bank
Da yake mayar da martani, lauyan bankin, Barrister Munir Barau Abdullahi, ya ce kwastomomin sun yi mu’amala ne da wata tsohuwar ma’aikaciyar bankin, ba kai tsaye da bankin ba, inda ya yi zargin cewa sun biya kuɗaɗensu ne cikin wasu asusu daban-daban maimakon na kansu a bankin.
Ya ce: “Sun yi mu’amala ne da wata tsohuwar ma’aikaciyar Jaiz Bank, amma ba su san cewa ba ta saka kuɗaɗensu a cikin asusunsu na bankin ba. Wannan shi ne ainihin abin da ya faru. Idan mutum ya bi ƙa’ida wajen ajiye kuɗinsa, to kuɗinsa yana cikin aminci. Wasu daga cikinsu sun gudanar da mu’amalolin ne bayan lokacin rufe banki, har ma a gidanta. Har yanzu shari’ar tana gaban kotu, kuma na yi mamakin ganin sun fito zanga-zanga.”
Barau ya ce an biya kuɗaɗen ne zuwa asusun ajiyar Habiba da mijinta a bankin, bisa wasu yarjejeniyoyin zuba jari da suka yi alƙawarin biyan ribar Naira 50,000 zuwa Naira 100,000 a kowane wata. A wani misali kuma, an yi alƙawarin biyan Naira 400,000 a duk wata kan jarin Naira miliyan 10, har sai da biyan kuɗaɗen ya tsaya.
Ya dage cewa bankin ba shi da alaƙa da waɗannan yarjejeniyoyi, kuma babu wata takardar hukuma da ke nuna cewa an biya kuɗaɗen cikin asusun bankin. Ya ƙara da cewa a lokacin binciken ’yan sanda, an gano tare da kwato takardun shaidar biyan kuɗi daga gidan Misis Abdulrahman.
Ya ce an gurfanar da Habiba da mijinta a gaban kotu bisa zargin damfara da haɗa baki wajen aikata laifi.
