Adalci ne sauya salon shugaba da mataimaki Musulmi zalla – Shugaban gamayya

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Takarar Musulmi zalla a shugabancin kasar nan, musamman al’amarin da ake ganin a jam’iyyar APC ba zai yiwu ba, ko da Amurka ba ta yi iƙirarin kashe Kiristoci a Nijeriya ba, watakila ma kisan mummuƙen siyasa suka fifita a kan kashe-kashen ’yan ta’adda, a cewar Malam Sham’unu Shykh Ali Musa Gabari, Shugaban Ƙungiyar Gamayyar Matasan Musulmi.

Domin ya yi nuni da cewa, tamkar yadda Majalisar shari’a ta Nijeriya ta gabatar da hujjojin da ya kamata a duba, sanna tsige shugaban Hukumar zaɓe ta INEC, haka yake ganin ya dace a yi shugaba da mataimaki Musulmi da kirista, saɓanin abin da muke gani na Jam’iyyar APC da ke kan doron ‘Muslim-Muslim Ticket, domin gudun ka da sauran jam’iyyu su kwaikwaya.’

Shugaban Gamayyar Matasan Musulmi ta Nadwatil Kubra Li Shababil Muslimin, ko Mega Assembly of Muslim Youth, ya yi nuni da cewa, ‘adalci shi ne turbar gina al’umma, har ta kasance cikin lumana.’ Saboda a cewarsa: “Na haƙaƙƙe Musulmi su suka fi yawa a faɗin ƙasarmu Nijeriya, amma matuƙar dai ana batun mabiya addinai ne, to Kiristoci su ne na biyu ko da kuwa mun ruɓanya su. Ko ba komai kamata ya yi a ce, Shugaba Musulmi ne, mataimakinsa kuwa ya kasance Kirista. Idan kuwa mara addini ma ake son bai wa matsayin, to lallai a nemi sahalewar Kiristoci.”

Shugaban ƙungiyar Gamayyar Musulmin, ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai bayan rufe bita ga masu wa’azin Azumin Ramadan da ke ƙaratowa, wanda aka gudanar a jami’ar Khairun ta Marigayi Khalipha Shykh Ishaq Rabi’u da ke Kani.

Dangane da batun matsalar cire shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa kuwa wato INEC, wanda Majalisar Shari’a ta Nijeriya ta jajirce a kai, ya ce a bi lamarin sannu a hankali, Musulmi ko Kirista su daina sukar wannan muhimmiyar buƙata, illa dai kawai a zauna a fahimci juna, ta yadda za a shawo kan matsalar, ta yadda za a kori gaba.

“Manyan malamai da ke cikin wannan majalisa ba za su yi gaban kansu don kawai suna son cire Kirista daga muƙaminsa. A’a, sai dai abin da suke nuni da shi cewa, ya taɓa aike wa Amurka da buƙatar kawo dauki don ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya, alhalin bai yi la’akari da halin da Musulmi suke ciki ba.

Don haka muke fatan idan an zauna an daddale hujjoji, Farfesa Josh Amuputan zai gane kuskurensa, kuma ya kiyayi gaba. Sai dai mu wannan matsalar ba za ta hana mu yin kira kan lallai a tabbatar da adalci, a kawar da jahilci, don ganin an sauya tsarin Shugaba da Mataimaki Musulmi zalla, musamman yadda muke ganin jam’iyya mai mulki ta APC ta yi,” inji shi.

Ya ma yi nuni da cewa lallai akwai buƙatar sauran jam’iyyu su daina marmarin tsarin shugabancin mabiya addini iri ɗaya a kasa irin Nijeriya. Saboda yana ganin Jam’iyyun Nijeriya su daina yin shugaban ƙasa da mataimaki musulmi ko Kirista zalla. “Wannan ba suka ba ce, sai dai ƙoƙarin tabbatar da adalci. Fatanmu dai al’umma ta fahimci wannan matsalar, ta hanyar dubi da idon basira,” in ji shi.

Malam Sham’unu ya ce: An taba yin shugaba da mataimaki Musulmi a Nijeriya, amma a zamanin mulkin soja, wato a 1983 zuwa 1984, inda Janar Muhammadu Buhari da Janar Tunde Idiagbon suka ja ragamar ƙasar nan. Sai dai a siyasa da ke kan tafarkin dimokuraɗiyya ba a tava ganin haka ba, sai a mulkin jam’iyyar APC.”

Ƙoƙarinmu dai, a daina saɓa wa dokokin ƙasa, sannnan a wuraren da suka ci karo da addininmu da al’adunmu, wajibi ne mu nemi a gyara. “A duk lokacin da za a yi wa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Garanbawul, sai mu matsa ƙaimin ganin an gyara al’amuran da suka ci karo da addininmu da al’adunmu. Uwa-uba tabbatar da adalci a tsakanin al’umma.”

Shugaban ƙungiyar Gamayyar ya ƙarkare da nuni da muhimmancin gyaran ta hanyar adalcin sauya salon tsarin shugabancin ƙasa na musulmi zalla. “Bayan an tabbatar da adalci, to mu ma sai mu jajirce, wajen ganin an yi mana namu muhimman buƙatu, waɗanda muke da tabbacin cewa ɗaukacin al’ummar ƙasar nan ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini ko na ƙabilanci ko na ɓangaranci kowa zai amfana.

By Babaji