Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da rashin gaskiya kan iƙirarin da take yi na cewa ana samun ƙaruwar samar da abinci a cikin gida, tana mai cewa rashin tsaro da gudun hijirar manoma musamman a Arewacin Nijeriya sun tabbatar da cewa wannan magana ba gaskiya ba ce.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta bayyana damuwa cewa gwamnati na “yaɗa labaran ƙarya kan saukar farashin abinci”, tana mai cewa wannan “manufar siyasa ce da ake amfani da ita wajen cutar da talakawa domin samun moriyar siyasa.”
“Akasin abin da gwamnati ke faɗa, gaskiyar abin da ke faruwa a ƙasa – kamar yadda manoma da talakawa ke tabbatarwa – shi ne gwamnati na yin sarrafa farashin abinci ne domin amfanin siyasa,” inji sanarwar.
Jam’iyyar ta bayyana cewa rahoton da ke nuna cewa farashin wasu kayan abinci ya sauka “ƙarya ce da ta samo asali daga amincewa da shigo da abinci daga ƙasashen waje cikin sauƙi,” wanda ta ce “ba hujja ba ce ta nasarar manufofi ko ƙaruwa a samar da abinci a cikin gida.”
Abdullahi ya ce: “Ko da yake hakan na iya kawo ɗan sauƙin farashi na ɗan lokaci, amma zai haifar da illa ga manoman cikin gida waɗanda ba za su iya gogayya da kayan da aka shigo da su ba, musamman saboda tsadar taki da rashin tsaro mai tsanani.”
Jam’iyyar ADC ta ce, duk da iƙirarin gwamnatin Tarayya cewa manufofinta na haifar da ƙarin samar da abinci a cikin gida, “gaskiya ita ce farashin da ake gani yanzu ya ragu saboda tsoron rikicewar kasuwa, ba wai saboda tsari mai kyau ko shiri ba.”
“Wannan duk yaƙin farfaganda ne,” inji sanarwar. “Abin da ke faruwa yanzu shi ne gwamnatinsu na yin sarrafa farashin abinci don amfanin siyasa na ɗan lokaci – domin a nuna kamar ana samun cigaba, alhali jama’a na ci gaba da wahala.”
Jam’iyyar ta kuma tambayi iƙirarin gwamnati na cewa ba ta fitar da abincin da ta shigo da shi zuwa kasuwa ba. “Idan ma za mu ɗan yi imani da wannan ƙaryar, tambayar ita ce: me yasa gwamnati ke ajiye abinci a ma’ajiyarta alhali jama’a na cikin yunwa? Wace irin gwamnati ce ke ɓoye abinci a lokacin matsanancin yunwa?”
ADC ta yi kira da a sake duba tsarin noma gaba ɗaya, tana mai cewa “gwamnati ta daina amfani da yunwa a matsayin makamin siyasa.”
Tun bayan cire tallafin man fetur a 2023, tattalin arzikin ƙasar ya shiga rikici, inda farashin abinci ya haura sakamakon tsadar sufuri da samarwa.
Sai dai daga farkon 2025, an samu sauƙi a kasuwa: farashin abinci ya ragu daga 21.87% zuwa 16.87% a watan Satumba 2025, wanda shi ne karon farko tun 2012 da aka samu koma-baya na farashin abinci da aka shigo da shi (-1.57%).
Haka kuma, hauhawar farashin kaya gaba ɗaya ta ragu zuwa 18.02% – mafi ƙanƙanta cikin shekaru uku.
Yanzu haka, buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 yana tsakanin N55,000 zuwa N63,000, maimakon an100,000 da ake sayarwa a baya; kwandon tumatir ya sauka daga ₦120,000 zuwa N35,000, yayin da garin rogo (garri) ya ragu daga N3,500 zuwa N2,000 ga kwantena lita 4.
Kayan abinci kamar masara, wake, albasa, barkono da dawa suma sun ragu da kashi 40 zuwa 55 a sassa daban-daban na ƙasar – duk da cewa ƙarfin siyan jama’a na ƙasa ƙwarai.
