Kotu ta ci tarar DSTV kan katse wa kwastoma sabis

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye da Masu Amfani da Kayayyaki ta ƙasa (FCCPC) ta bayyana gamsuwa da wasu sabbin hukuncin kotu da suka ƙarfafa kare haƙƙin kwastamomi a faɗin Nijeriya, tana mai cewa, wannan cigaba ne mai ƙarfi wajen tabbatar da gaskiya da ladabi a kasuwar Nijeriya.

A wata sanarwa da darektan hulɗa da jama’a na hukumar, Ondaje Ijagwu, shugaban hukumar Tunji Bello ya yaba wa kotuna bisa yanke hukunci da suka tabbatar da aiwatar da dokar Federal Competition and Consumer Protection Act (FCCPA) ta 2018, tare da ƙarfafa ’yan ƙasa su nemi adalci idan an tauye musu haƙƙi.

A cikin hukuncin farko daga Babbar Kotun Jihar Legas, Mai Shari’a R. O. Olukolu ya umarci kamfanin Multichoice Nigeria Limited mai mallakar DStv da ya biya wani kwastoma, Ben Onuora, diyya ta naira miliyan biyar, bayan kamfanin ya katse masa sabis duk da cewa ya riga ya biya kuɗi.

Kotun ta bayyana cewa katsewar sabis ɗin ta saɓa wa doka, kuma ta jawo wa wanda abin ya shafa da iyalinsa ɓacin rai.

A wani hukunci daban kuma, Babbar Kotun Jihar Enugu ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a C. O. Ajah, ta bayyana tsarin kamfanin Peace Mass Transit na “babu mayar da kuɗi bayan an biya” a matsayin ba bisa doka ba. Kotun ta ce tsarin ya take sassan 120, 104, da 129(1) na dokar FCCPA, waɗanda ke tabbatar da haƙƙin mabukata su karɓi kuɗinsu idan ba a samu sabis cin da aka biya ba.

Kotun ta kuma umurci Peace Mass Transit ta biya N500,000 ga wani fasinja, Mista Tochukwu Odo, wanda aka hana mayar da kuɗinsa bayan tafiyarsa ta lalace ba tare da ya isa inda yake so ba.

Shugaban FCCPC, Tunji Bello, ya ce waɗannan hukuncin suna nuna ƙarfin dokar FCCPA da kuma shirye-shiryen kotunan ƙasar wajen kare haƙƙin masu amfani da sabis.

Ya yaba wa waɗanda abin ya shafa bisa bin hanya ta doka wajen neman adalci, maimakon komawa tashin hankali ko hayaniya a kafafen sada zumunta, yana mai bayyana cewa hukumar na da hanyoyi da dama da ake iya kai ƙara, ciki har da portalin yanar gizo, imel, da kuma ofisoshi a jihohi daban-daban.

Bello ya kuma bayyana cewa tsakanin watan Maris da Agusta na shekarar 2025, hukumar ta taimaka wajen maido wa masu amfani da sabis sama da naira biliyan goma (N10bn) da aka karɓa daga kamfanoni a sassa fiye da 30 na tattalin arziƙin ƙasa — abin da ya bayyana a matsayin hujja cewa tsarin kare masu amfani da sabis na ƙara samun tasiri.

Ya ce, “Yanke hukunci daga kotuna yana cika ayyukan hukumar wajen tabbatar da ladabi a kasuwa, tare da isar da sako ga duk masu karya haƙƙin mabukata cewa akwai hukunci na gaske da ke jiransu.”

A ƙarshe, Bello ya shawarci mabuaata da su ci gaba da bayar da rahoton duk wata rashin gaskiya daga masu ba da sabis, tare da tabbatar musu cewa hukumar za ta ci gaba da kare su, inganta ma’aunin sabis, da tabbatar da gasa ta gaskiya a kasuwa.

Hukumar FCCPC wacce aka kafa ƙarƙashin dokar FCCPA ta 2018, ita ce babbar hukumar ƙasa da ke da alhakin kare haƙƙin mabuƙata da kula da gasa tsakanin kamfanoni, domin tabbatar da gaskiya, kau da cin zarafi, da tabbatar da ɗawainiya tsakanin masu samar da kayayyaki da masu amfani da su.

By ukarofi