An cire Nijeriya daga jerin ƙasashe masu aikata almundahanar kuɗaɗe

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya bayyana cewa, an Nijeriya daga jerin ƙasashen da aka fi saka wa ido saboda yawan aikata zamba da kuma halasta kuɗaɗen haram a duniya.

ƙungiyar kula da irin waɗannan laifuka ta ‘Financial Action Task Force’ (FATF) mai hedikwata a Faransa ta bayar da sanarwar cire ƙasashen biyu mafiya girman tattalin arziki a Afirka yau Juma’a bayan taronta.

Ta kuma cire ƙasashen Burkina Faso da Mozambiƙue daga jerin nata na ƙasashen da take bayar da shawarar tsaurara saka ido a kan su saboda ayyukan masu damfara da halasta kuɗin haram.

A shekarar 2023 ne aka saka Nijeriya da Afika ta Kudu ciki jerin, kuma FATF ta ce Nijeriya ta ƙarfafa wa hukumomi gwiwar yin aiki tare.

Wata sanarwa daga fadar shugaban Nijeriya ta ce Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana matakin a matsayin “gagarumin cigaba a yunƙurin Nieriya na gyaran tattalin arziki da kuma inganta ayyukan ma’aikatun gwamnati.”

Nijeriya dai ta shiga jerin ƙasashen da ake sanya ido tun a Fabrairu 2023 saboda raunin aiwatar da doka, rashin haɗin kai tsakanin hukumomi, da kuma rashin gaskiya a wasu harkokin kuɗi.

Shugaba Tinubu ya ce, gwamnatinsa ta ɗauki wannan ƙalubale a matsayin kira zuwa aiki, inda ya umurci hukumomin da abin ya shafa su aiwatar da gagarumin sauye-sauye.

A ƙarƙashin jagorancinsa, Hukumar Binciken Bayanai ta Kuɗi ta ƙasa (NFIU) tare da Ofishin Lauyan Gwamnatin Tarayya, da ma’aikatun Kuɗi, Shari’a da Cikin Gida, suka jagoranci aiwatar da gyare-gyare na doka da tsarin aiki domin cika ƙa’idojin FATF.

Tinubu ya yaba da jajircewar Darakta-Janar ta NFIU, Hajiya Hafsat Bakari, da tawagarta, bisa “ƙwazon da suka nuna wajen aiwatar da sauye-sauye cikin lokaci,” wanda ya ba Nijeriya yabo a idon duniya wajen yaƙi da manyan laifukan kuɗi.

Bakari, wadda ta jagoranci aikin gyaran, ta tabbatar da cire sunan Nijeriya daga jerin ƙasashen da ake sanya ido, tana cewa, “FATF ta cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke ƙarƙashin ƙarin sa ido – wannan babban tarihi ne a yaƙi da manyan laifukan kuɗi, kuma shaida ce ga jajircewarmu wajen bin ƙa’idojin duniya.”

Ta bayyana cewa muhimman sauye-sauyen da suka kai ga wannan nasarar sun haɗa da, aiwatar da dokokin Money Laundering (Preɓention and Prohibition) Act, 2022 da Terrorism (Preɓention and Prohibition) Act, 2022; kafa da fara amfani da Beneficial Ownership Register; da kuma ƙarfafa sa ido kan wasu cibiyoyi da ke da alaƙa da harkokin kuɗi.

Haka kuma, ta ce an ƙarfafa ikon hukumomin leƙen asiri da na tilasta bin doka wajen gano, bincike da gurfanar da masu laifin kuɗi, tare da inganta haɗin gwiwar ƙasashen waje.

Bakari ta gode wa Shugaba Tinubu bisa jagoranci mai hangen nesa, tare da yabawa Majalisar Dokoki, ɓangaren shari’a, da masu zaman kansu, tana kira da a ci gaba da riƙe wannan tafarki domin tabbatar da bin ƙa’idojin duniya.

A wannan taron na FATF, ƙasashen Afirka ta Kudu, Mozambiƙue, da Burkina Faso suma an cire su daga jerin bayan samun ci gaba a tsarin kuɗaɗensu.

Masana sun ce fitar Nijeriya daga wannan jerin zai inganta mu’amalar kasuwanci da ƙasashen waje, jawo jarin waje, da karfafa amincewar masu zuba jari da tattalin arzikin ƙasa.

Shugaba Tinubu ya kammala da cewa, “Wannan sabon babi ne a tafiyar gyaran tsarin kuɗi na Nijeriya. Za mu ci gaba da ƙarfafa sauye-sauyen da aka kafa, da haɗin kai, domin gina tsarin kuɗi wanda ’yan Nijeriya da duniya za su yarda da shi.”

By ukarofi