Addinina ya koyar da ni yin adalci ga kowa -Tinubu

Spread the love

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed ya jaddada aniyarsa ta yi wa kowa adalci a mulkinsa tare da tabbatar da ya haɗa kan ‘yan Nijeriya da samar da walwala ga ƙasar da ‘ya’yanta.

Da yake jawabi bayan kammala sallar Juma’a a babban masallacin Ansar-Ud-Deen da ke Suruleren, Jihar Legas, a ranar Juma’a, Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta ɓullo da su na da nufin samar da tsayayyen tushe da ‘ya’ya da jikokin ‘yan Nijeriya za su mora.

Shugaba Tinubu, wanda ya bi sahun al’ummar Musulmi wajen gudanar da addu’o’in bikin cikar ƙungiyar Musulmi ta Ansar-Ud-Deen Society of Nigeria shekara 100 da kafuwa, ya yaba wa ƙungiyar bisa hidimar da take yi wajen yaɗa addinin Musulunci da kyautata rayuwar bil’adama, da karɓan hakkin waɗanda aka zalunta.

Ya kuma yi kira ga ‘yan uwa da su ci gaba da jajircewa kan manufofinsu na ciyar da ilimin ‘yan ƙasa gaba, tare da bunƙasa kyawawan halaye da zamantakewar al’ummar musulmi.

Shugaban wanda ke hutun ƙarshen shekara a jihar ta Legas ya ce baya da rage kashi 50 cikin 100 na farashin zirga-zirgar a tsakanin jihohi a faɗin ƙasar nan da gwamnatinsa ta yi, ya bayar da umarnin biyan kuɗaɗen alawus-alawus na masu cin gajiyar N-Power.

“Wannan na daga cikin matakan da muke ɗauka duk a ƙoƙarin rage radadin da ‘yan Nijeriya ke fama da shi a kakar bukukuwan shiga sabuwar shekara.

By Editor