Daga BASHIRI ISAH
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya ƙaddamar da aikin gyaran College of Health Sciences and Technology da ke tsafe.
Ƙaddamarwar wadda ta gudana a ranar Juma’a na mazaunin ɓangare ne na ƙudurin inganta fannin ilimin jihar da Gwamnan ke da shi.
Aikin gyaran kwalejin ɓangare ne na shirin NG-CARES na Bankin Duniya wanda aka assasa don kyautata rayuwar ‘yan karkara ta hanyar gyara musu abubuwan more rayuwa da ke yankunansu.
Kakakin Gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa, aikin gyaran College of Health shi ne na farko a jerin ayyukan gyara wasu zaɓaɓɓun makarantu da za a gudanar a sassan jihar.
Idris ya ƙara da cewa, sa’ilin da yake jawabi yayin ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal ya jaddada aniyarsa ta inganta fannin ilimin Zamfara.
“Muna da niyar sarrafa kuɗin NG-CARES daidai da dokoki da tsare-tsaren Bankin Duniya ta yadda za a bunƙasa makarantun gwamnati sannan mutanemu su samu aiki.
“Ina da ƙwarin gwiwar mutanenmu za su ci moriyar wannan dama yadda ya kamata. Mu mutane ne masu aiki tuƙuru tare da bai wa harkar kwasuwanci muhimmanci.
“A matsayinmu na gwamnati, mun jajirci wajen yi aiki gwargwado iko kuma cikin yardar Allah, domin tabbatar da walwala da kuma samar da harkokin bunƙasa tattalin arziki don amfanin al’ummar jihar baki ɗaya,” in ji Gwamna Lawal.
