Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafar Afrika (CAF) ta amince da sunayen tawagar ’yan wasan wucin gadi na Super Eagles ta Nijeriya da za su taka leda a gasar kofin Afrika ta 2023 kamar yadda kocin ƙungiyar, Jose Peseiro ya miƙa mata.
CAF ta tabbatar da jerin sunayen kamar yadda aka bayyana a shafin yanar gizonta a ranar Laraba.
Ana sa ran Peseiro ya gabatar da cikakkiyar tawagarsa ta ƙarshe ga hukumar ta CAF kafin wa’adin da aka ɗiba ya ƙare a ranar 3 ga watan Janairu.
A cikin jerin sunayen akwai ’yan wasa uku da ke taka leda a cikin gida – Ojo Oluwasegun (Enyimba FC), Christian Nwoke (Sporting Lagos FC) da Obasogie Amas (Bendel Insurance).
Bayan hukunci da kwamitin shirya gasar CAF na AFCON ya yanke, za a ba wa dukkanin ƙungiyoyi 24 izinin shigar da jerin ’yan wasa 27 na ƙarshe, wanda ya zarce 23 da aka buga gasar a baya.
Za a soma gasar ce daga ranar 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairu, 2024, a garuruwan Abidjan, Bouake, Korhogo, San Pedro da Yamoussoukro na ƙasar Ivory Coast.
A ɗaya ɓangaren kuma, masu karvar baƙuncin gasar kofin nahiyar Afirka a Ivory Coast, sun ce an kammala shirya yadda za a gudanar da wasan, tare da tabbatar da cewa an tsaurara matakan tsaro, domin kaucewa abin da ya faru a ƙasar Kamaru a shekarar 2021.
Wannan zai kasance karo na biyu kenan da ƙasar ta karɓi baƙuncin gasar, bayan wanda ta karɓa a shekarar 1984, lokacin da ƙassashe takwas ne ke buga gasar maimakon 24 da aka koma yi a yanzu.
Za a fara gasar ne daga ranar 13 ga Janairu zuwa 11 ga Fabrairu, inda Senegal da ke kare kambunta bayan ta doke Masar a bugun daga kai sai mai tsaron gida a ƙasar Kamaru, ke duba yiwuwar sake ɗaukar wannan kofi a karo na biyu a tarihinta.
An zuba jarin kusan sama da dala biliyan ɗaya, domin gyara hanyoyin da ke gaɓar ruwa, musamman hanyar da ta haɗa birnin Abidjan da San Pedro, domin sauƙaƙawa ‘yan kallon da ke son halartar biranen da aka ware.
Yayin da matsalar sha’anin tsaron da ake samu daga masu tayar da ƙayar bayan da ayyukanssu suka yi ƙamari a makwabtan ƙasashe irin Mali da Burkina Faso, hukumomin ƙasar na cigaba da tsaurara matakan tsaro, domin cire fargaba a zukatan ‘yan kallo da ke cike damuwa kana bin da ya faru a birnin Yaounde, shekaru biyu da suka gabata.
A wancan lokacin an samu mutuwar mutum takwas, inda gommai suka jikkata, bayan hatsaniyar da aka samu a wasan da ya wakana tsakanin Kamaru da Comoros.
Youssouf Kouyate, darakta janar na rundunar ‘yan sandan Ivory Coast, ya shaidawa AFP cewa, an tsaurara matakan tsaro a dukkanin filayen wasa shida da aka ware, domin kwantar da hankalin ’yan kallo sama da miliyan guda da dubu 5000 da ake sa ran za su halarci kallon wasan.
Sama da sojoji da ‘yan sanda 17 aka girke, haɗi da ma’aikatan filin wasa 2,500, domin tabbatar da cewa na gudanar da wannan gasa cikin kwanciyar hankali.
