Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Ma’aikatar lafiya ta Jihar Kebbi ta sha alwashin ɗaukar matakin kai ziyarar bazata a manyan asibitocin da ke faɗin jihar.
Kwamishinan Lafiya na jihar Honarabul Yunusa Musa Isma’il ne bayyana haka a wata ziyara da ya kai a asibitin garin Kamba a ƙaramar hukumar mulki ta Dandi.
Kwamishinan ya ce yin haka zai zaburar da ma’aikatan wajen mayar da hankali ga ayyukansu musamman waɗanda ke wasa ko kuma rashin zuwa wajen aiki, bayan wannan kuma don su je su gane wa idonsu abubuwan da ke faruwa a asibitoci don ɗaukar matakin da ya dace.
Irin wannan ziyarar ta ba-zata tana bai wa ma’aikata ƙwarin gwiwa wajen aiwatar da ayyukansu musamman a ɓangaren lafiya wanda yana daga cikin ɓangarorin da ke da muhimmanci a rayuwa.
Ya ja hankalin ma’aikatan da su mayar da hankali wajen aikinsu duk da kasancewar wannan gwamnatin tana sane da ƙarancin ma’aikatan lafiya musamman a manyan asibitocin da ke faɗin jihar wanda yanzu haka gwamanti tana iya ƙoƙarinta wajen ganin ta warware bakin zaren don samun wadatattun ma’aikata.
