Adeleke ya jinina wa Tinubu kan sahihin zaɓe a Osun, ya sabunta goyon bayansa gare shi a zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun ya jinina wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa abin da ya kira da “sahihin zaɓen gwamna” da aka gudanar a jihar, yayin da ya kuma jaddada goyon bayansa ga shugaban na neman a sake zaɓar sa a karo na biyu a zaɓen 2027.

Adeleke ya bayyana haka ne a ranar Lahadi jim-kaɗan bayan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sanar da sh ia matsayin wanda ya lashe zaɓen, wanda aka gudanar a ranar Asabar 15 ga Agusta, 2026, lamarin da ya ba shi damar koma wa kan karagar mulkin jihar a karo na biyu.

Ya ce, musamman Shugaba Tinubu ya kira sa ta wayar tarho ya taya shi murnar lashe zaɓen, yana mai bayyana matakin shugaban a matsayin ƙoƙarin ƙarfafa lamuran dimukraɗiyya a sassan Nijeriya.

“Ina cikin matuƙar farin ciki, Da fari, Ina godiya ga Ubangiji Maɗaukaki kan abin da ya faru a yau. Nasara ce ga dimukraɗiyya a Nijeriya,” inji Adeleke.

Adeleke ya kuma jaddada aniyarsa ta mara wa takarar Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027 da ke tafe domin a sake zaɓar sa a karo na biyu a kujerar shugabancin Nijeriya.

Waɗannan kalamai na nuna cewa akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin jagororin biyu musamman bisa la’akari da ziyarar da Adeleke ya kan kai wa Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da kiran waya da ke wakana a tsakaninsu.

Tinubu dai shi ne jagoran jam’iyyar APC yayin da Adeleke kuma ya tsaya takarar gwamnan Osun a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Accord Party (AP) bayan ficewa da PDP.

By Babaji

Leave a Reply