
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu saɓani a yayin wani zama da aka gudanar tsakanin shugabannin Majalisar Dattawa game da lokacin tafiya hutun wata biyu na majalisa da aka saba yi kowace shekara.
A yayin zaman ne muryoyi suka shaida wa SaharaReporters cewa an samu saɓanin ne a tsakanin shugabannin a lokacin da ake ƙoƙarin cimma matsaya kan batun shirin ɗage tafiya hutun.
Lamarin, wanda ya auku a ranar Laraba a yayin wata ganawar sirri, ya sa an yi musayar kalamai cikin fushi tsakanin Shugaban majalisar Godswill Akpabio da kuma jagora a majalisar, Opeyemi Bamidele, inda suka kusa bai wa hammata iska.
An ruwaito cewa, a yayin zaman ne Sanata Ali Ndume ya soki jagorancin majalisar saboda a cewarsa tun kafin zaman ya dace su cimma matsaya gabannin gabatar da batun ga mambobi.
Hakan ya biyo bayan Opeyemi ya soki tsarin shugabancin Akpabio a majalisar, lamarin da ya sa Ndume ya ce akwai buƙatar su nuna dattako a matsayinsu na dattawan ƙasa.
Wannan shi ne karo na biyu da ake samun rahoton sanatocin biyu sun samu saɓani a tsakanin su tun a watan Nuwamba 2024, saidai daga baya an ƙaryata labarin faruwar hakan.
