
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai halarci taron tsare-tsaren abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya karo na biyu, wanda za a yi a Addis Ababa, Babban Birnin ƙasar Habasha.
Za gudanar da taron ne daga ranar 27 zuwa 29 ga watan Yulin nan kamar yadda Kakakinsa Stanley Nkwocha ya bayyana a wata takarda, ranar Lahadi.
An shirya babban taron ne da haɗin-gwiwar gwamnatocin Habasha, Italiya da Majalisar Ɗinkin Duniya inda za a tara shugabannin ƙasashen duniya.
Za a yi nazari game da nasarorin da aka cimma a zangon farko da ƙaddamar da tsare-tsaren inganta harkokin samar da abinci tun a shekarar 2021.
Shettima na ɗaya daga cikin shugabannin ƙasashe da manyan jami’an gwamnati da za su halarci taron, inda zai bada ba’asi kan masana’antar samar da ƴaƴan ganyen shayi na ‘coffe’ da yadda Nijeriya ta samu cigaba wajen inganta lamuran samar da abincin.
Haka kuma, kakakin mataimakin shugaban ƙasar ya ce, Shettima zai shiga tattaunawa da ministoci jagororin hukumomin fannin noma don tattauna dabarun inganta abinci da harkokin zuba jari acikinsu.
Ana sa ran zaman zai taimaka wajen samar da yanayi mai kyau na samar da abinci da tabbatuwar ɗorewarsa acikin al’ummar ƙasashen duniya.
