
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An shiga halin zaman ɗar-ɗar acikin ɗaliban Makarantar Lauyoyi ta Nijeriya bayan zargin ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ɗalibai guda shida na makarantar akan hanyar Benuwai zuwa Taraba.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya auku ne a daren ranar Asabar wayewar Lahadi, wanda ya rutsa da ɗaliban waɗanda suka taho daga Onitsa a jihar Anambara domin koma wa karatunsu a reshen makarantar dake Yola, Jihar Adamawa.
Ɗaya daga cikinsu mai suna Damilare Adenola ta tabbatar wa jaridar NewsPoint Nigeria faruwar al’amarin inda ta ce abokan karatunta guda shida aka yi garkuwa da su a yayin tafiyar.
Waɗanda suka shiga hannun ƴan bindigar sun haɗa da Rev. Ernest Okafor, Thomas Sankara,
Ogbuka Fabian, Nwamma Philip, Okechukwu Obadiegwu, Obalem Emmanuel da kuma Obiorah David.
Lamarin ya auku ne a kan iyakar Wukari dake Taraba da jihar Benuwai, inda ayyuka ƴan bindiga ya yi ƙamari ciki har da garkuwa da mutane, fashi da hare-hare daga makiyaya.
