‘
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Aƙalla mutane 35 da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda dake Jihar Zamfara ‘yan ya’adda suka halaka bayan sun karɓi sama da Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.
Wani mazaunin yankin a wata hira ta wayar tarho da Blueprint Manhaja mai suna Lawali Muhammad Banga, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da mutane 53 a ƙauyen su watannin baya inda suka buƙaci Naira miliyan ɗaya ga kowane mutum a matsayin kuɗin fansa domin su sako mutanen nasu.
A cewarsa, mutane 18 ne kawai ‘yan ta’addan suka sako da ransu, daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, yayin da mutum 35 suka kashe.
“Waɗannan ‘yan ta’addan sun kashe mazajenmu 34 da mace ɗaya yayin da suke hannun su, kuma mun samu rahoton faruwar hakane daga mutanen mu 18 da aka sako su daga hannun Waɗannan ‘yan ta’adda.”
“Waɗanda aka sako da rai sun shaida mana cewa sauran waɗanda aka yi garkuwa da su 35, ‘yan ta’addan sunyi masu yankan rago ɗaya bayan ɗaya bayan mun biya kudin fansa sama da Naira miliyan 50”. Yace
Malam Lawali Muhammad Banga ya bayyana cewa a halin yanzu yankin na ƙarƙashin ikon ‘yan ta’adda ne, inda ya ce an kori ƙauyuka da dama da ke kewaye da ƙauyen Banga sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da gwamnatin tarayya da su kawo musu ɗauki ta hanyar baza sojoji a yankin domin daƙile ‘yan ta’addan da ke addabar yankin domin a samu zaman lafiya.
