Gwamnatin Gombe ta nemi taimakon masarautar Gombe wajen aiwatar da dokar hana cin zarafi

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

A yunƙurin da gwamnatin Jihar Gombe ke yi na magance cin zarafin mata da yara, ma’aikatar harkokin mata ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Asma’u Mohammed Iganus ta gabatar da kundin dokar hana cin zarafi (GBV) ga mai martaba sarkin Gombe, Alhaji Dr. Abubakar Shehu Abubakar III, domin samun cikakken goyon bayan sarakunan gargajiya wajen tabbatar da aiwatar da dokar a ƙasa.

Taron da aka gudanar a zauren ƙaramar hukumar Gombe ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, inda aka tattauna hanyoyin da za a bi don ganin an kawar da duk wata ɗabi’a da ke haifar da cin zarafi musamman ga mata da ƙananan yara.

Da take gabatar da jawabi a wajen taron, kwamishinar mata Asma’u Iganus ta bayyana cewa, “sarakunan gargajiya na da matuƙar muhimmanci wajen canza tunani da ɗabi’un da ke janyo cin zarafi.

Tare da goyon bayansu, zamu samu nasarar tabbatar da wannan doka cikin sauƙi.”

A lokacin da yake karɓar kwafin dokar a madadin sarkin Gombe, Dan Lawan Gombe, Dr. Sani Adamu Jauro, ya tabbatar da cewa masarautar Gombe na maraba da wannan yunƙuri.

“Mai Martaba yana tare da wannan doka, kuma masarauta za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnati da ƙungiyoyin al’umma domin kare haƙƙin mata da yara,” in ji shi.

Shugaban kwamitin majalisar dokokin Jihar Gombe kan harkokin mata, Mista Gabriel Galadima, ya bayyana cewa dokar tana cikin matakin aiwatarwa tun bayan da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya rattaɓa hannu a kanta.

Ya ƙara da cewa, “Wannan doka ba ta bar kowa a baya ba sani ba sabo kuma ba wanda zai wuce ta.”

Shima Shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barr. Sani Ahmad Haruna, ya bayyana goyon bayansa ga dokar, tare da alƙawarin wayar da kai a tsakanin jama’a, tallafawa waɗanda abin ya shafa, da kuma ƙarfafa sauyin ɗabi’u a cikin al’umma.

Wannan yunƙuri, wanda ke samun goyon bayan ƙungiyar UN Women, na nuna haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma wajen yaƙar cin zarafin jinsi da tabbatar da adalci ga dukkannin ‘yan ƙasa.

By ukarofi