Kogi: Tashar Radio Nigeria ta ɗauke bayan ƴan fashi sun farmake ta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tashar Rediyo Nijeriya mai aiki a zangon FM 101.5 a Jihar Kogi ta samu tsaiko bayan da wasu ƴan fashi suka kai wa tuƙullumar watsa labaranta mai tsadar miliyoyin kuɗaɗe hari, inda suka sace wasu daga kayayyakin ofishinta.

Janar Manaja ta tashar, Momoh Jimoh Adeiza a wani saƙo da aka fitat, ta ce lamarin ya auku ne a safiyar ranar Asabar.

An ruwaito cewa, ɓarayin sun shafe tsawon sa’o’i uku suna fashi a gidan rediyon.

Adeiza ta shaida wa manema labarai cewa sun tashi da safe kwatsam suka tarar da an lalata ofishin nasu ba tare da iya gano waɗanda suka aikata ba.

A lokacin da ɓarayin suke je fashin, sun samu damar ɗaure masu gadin da ke aikin tsaro a ofishin, lamarin da ya sa suka ci karensu ba babbaka da tafiya da wasu kayan aikin watsa labarai.

Janar Manajar ta kuma kirayi hukumomin da ke da alhakin kula da harkokinsu da su gaggauta kawo musu ɗauki.

A wani labarin, Gwamnatin jihar ta yi alla-wadai da lalata kayayyakin aikin gidan rediyon.

Kwamishinan Labarai na jihar, Kingsley Femi Fanwo a wata sanarwa, ya ce gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da kamo waɗanda suke da hannu a ɗanyen aikin tare da gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin doka.

By Babaji