Akwai jituwa tsakanin ƙungiyar NATA da GAATN a Gombe – Injiniya Mustapha

Daga WAKILINMU

Shugaban sabuwar ƙungiyar makanikai da ƙere-ƙere ta Jihar Gombe, wato ‘Guild of Automobile and Allied technicians’ (GAATN), Injiniya Mustapha  Hassan, ya ƙaryata zargin da ake yi na cewa ƙungiyar ta su ta valle ne daga uwar ƙungiyarsu ta NATA saboda rashin jituwa a tsakanin NATA da GAATN.

A hira da manema labarai a Gombe cikin makon jiya, injiniya Mustapha yayi muni da cewa, babu wani rashin jituwa, illa kawai sun kafa GAATN ne don ƙara faɗaɗa harkar makanikanci da ƙere-ƙere a faɗin Jihar Gombe, musamman ganin yadda matasa ke shigowa sana’ar walda, ƙira, balkanaiza, aikin lantarki da sauran su.

‘’To ka ga dole mu ƙara ƙaimi, muga  mun faɗaɗa harkokin ƙungiyar saboda yadda waɗannan matasa suka yunƙuro da neman abun dogaro don taimakon kansu, kuma wajibi ne mu ƙara musu ƙarfin gwiwa. Saboda haka, ai kafa ƙungiya GAATN, kamar wani ƙarin ci gaba ne a Jihar Gombe, amma ba don wani hamayya ko rashin jituwa ba’’, inji shi.

Ya ce, a yanzu haka, sun samu mambobi da suka yi rijista da  ƙungiyar mutum sama da 2,500  a faɗin jihar Gombe, yana mai ƙarawa da cewa, shugabannin baya a uwar ƙungiyar, basu tsinana ma ta komai ba, in banda rarrabuwar kawuna da suka kawo a tsakanin mambobi, kuma shugabancin ba ta da wani tasiri.

Yanzu, a cewar shi, banda ƙere-ƙere, suna kuma sayar da kayayyakin Babura, motoci harda na tirakta, kuma suna iya gyaran duk wani nau’in inji kuma suna da kwastomomi daga ko ina a cikin Arewa, yana mai cewa, ƙungiyar ta GAATN, ita ce gaba akan duk wata ƙungiyar a Arewa maso Gabashin Nijeria.

A nan, sai Injiniya Mustapha, ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa wa  ƙungiyar saboda irin alfanun take da shi a cikin Jihar, musamman wajen baiwa al’umma aikin yi, yawancin su kuma matasa.

Ya kuma jinjina wa Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya akan ci gaban da ya kawo wa Jihar cikin shekaru uku.

Shi dai Injiniya Mustapha ɗan asalalin Gombe ne an haife shi ne a garin Jos, Jihar Filato.

Ya yi karatun difloma da babban difloma a makarantar horon malamai (NTI) ta ƙasa da ke Kaduna da kuma digirin shi ta fannin duk dai a NTI ɗin kafin daga bisani ya yi babbar digiri a jami’ar tarayya (NOUN).

Shine kuma shugaban kamfanin Mustapha Turbo Charger (MTC) da ke Gombe.

Yana da ma’aikata kusan 30 a kamfanin nashi, kuma kwanan baya ne aka ji shugaban NATA na Jihar Gombe, Injiniya Ahmed Waziri yake furuncin cewa, wasu mambobin  ƙungiyar sun fice suka kafa sabuwar ƙungiyar su mai suna GAATN ce,  saboda rashin jituwar da neman shugabancin ƙungiyar ko ta halin kaka ya haddasa.

‘’Sun kafa sabuwar ƙungiyar ce saboda son shugabanci ba bisa tsari ba, da kuma son kai ba don ci gaban ƙungiya ba’’, inji Injiniya Ahmed.