Ya kamata Gwamnatin Kano ta duba yunƙurin cutar da al’ummar Dakata – Arewa Media Writers

Daga WAKILINMU

Ƙungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani ‘Arewa Media Writers’, ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Comr Abba Sani Pantami, da Shugaban ƙungiyar reshen Jihar Kano, Comr Umar Kabir Dakata, tana kira ga gwamnatin Jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki da su duba yunƙurin cutarwa da ake ƙoƙarin aikata wa ga al’ummar unguwar Dakata da ke cikin kwaryar Jihar Kano.

Arewa Media Writers ta samu labari daga al’ummar wannan yanki cewa, rana tsaka aka wayi gari an zo an gina wani katafaren waje cikin sirri, duk da ƙoƙarin da suke wajen tsaftace anguwar daga munanan ɗabi’u musamman shaye-shaye da sauran harkokin Sharholiya ga matasan yankin.

A binciken da ƙungiyar, ta samu labarin cewa mamallakin wajen ya yaudari waɗanda ya sayi wajen a hannunsu ne da kuma Dagacin Anguwar Dakata, Alhaji Salisu Ibrahim Zubairu, kan cewa gidan abinci zai buɗe a wannan waje, hakane ya ba shi dama ya dinga aikin cikin sirri ba ayi aune ba rana tsaka sai gani aka yi an yi fanti kamar yadda za a gani a cikin hotuna.

Bayan kammala bincike na tsanaki da Ƙungiyar ‘Arewa Media Writers’ ta yi game da wannan mummanan lamari, a ƙarshe tana mai miƙa ƙoƙonta a madadin al’ummar anguwan Dakata zuwa ga gwamnatin jihar Kano, da duk masu ruwa da tsaki kan su yi duba zuwa ga wannan aiki, tare da dakatar da varnar nan take, domin ceto tarbiyar al’ummar wannan yanki.

A ƙarshen ƙungiyar ta ce, “muna fatan mai girma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam) zai sharewa al’ummar Anguwar Dakata hawaye game da wannan babban iftila’in da ya faɗo unguwar don ganin an tseratar da tarbiyar matasan unguwar.