Mai shekaru 101 ya koka kan ƙwace filayensa da wani babban mutum ya yi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wani dattijo mai shekaru 101 da haihuwa mai suna Alhaji Shehu Jibiya ya koka kan abin da ya kira fin ƙarfi tarebda zargin wani mainsuna Buzu, wanda yaro ne ga Alƙalin-alƙalan jihar Zamfara, Hajiya Kulu da yin kutsawa cikin filayen sa guda 20 tare da qwace masa a Gusau babban birnin jihar.

A cewar sa, Buzu ya yi amfani da rigar uwar gidansa ne kimanin shekaru 20 da suka gabata inda ya ƙwace filayensa da ya ce ya saya kuma yana da dukkan takardun filayen.

Alhaji Shehu Jibiya ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Blueprint Manhaja a ranar Talata a Gusau.

Ya ƙara da cewa an gabatar da ƙarar a gaban kotu har sau shida, wanda tun lokacin shekaru ashirin kenan dukkan alƙalan da suka yi shari’ar suna yin watsi da ƙarar ba bisa ƙa’ida ba.

“Mun zauna sau shida daban-daban a gaban kotuna kuma na gabatar da shaiduna a gaban waɗannan kotunan amma abin takaici su alƙalan da suka gudanar da shari’ar sun yi watsi da ƙarar tawa saboda kawai ni ba ni da gata sai Allah.”

Tsohon ya yi nuni da cewa tun da farko ya tuntuɓi Gwamna Bello Mohammed Matawalle kan lamarin kuma ya yi masa alƙawarin shiga tsakani domin gyara masa lamarin, inda ya koka da yadda ya kasa ganin gwamnan domin tunatar da shi.

“Na yi magana da Gwamna Matawalle a hukumance a farkon wannan shekarar, kuma ya yi min alƙawarin zai sa baki, amma ban samu sauƙin sake ganinsa ba,” inji shi. 

Ya kuma bayyana cewa ya kwashe shekaru 60 yana zaune a Gusau kuma yanzu ya cika shekara 101 a duniya, inda ya yi kira ga Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam da sauran masu ruwa da tsaki da su kawo masa ɗauki don tabbatar da adalci a kan lamarin.

“Ina kira ga Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Ministan shari’a, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da su sa baki cikin gaggawa don magance matsalata”, ya ce.

Sai dai wakilinmu bai samu damar jin ta bakin Buzu da ake zargin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.