Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse
Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Hussaini Adamu ya yi kira ga al’ummar masarautarsa da su kasance masu son zaman lafiya da kuma bin doka da oda a yankinsa.
Mai Martaba Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da al’ummar Ƙaramar Hukumar Gwiwa a ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙaramar hukumar, Sale Ahmed Zauma suka ziyarci fadarsa. Ya bayyana muhimmancin da zaman lafiya yake da shi ga ci gaban tattalin arziki.
Alhaji Najib Hussani Adamu, ya shawarci matasa da su kasance masu kyawawan ɗabi’u da kuma neman ilmin addinin Musulunci da na zamani da nufin samun al’umma tagari.
Da ya ke bayaninsa, Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Gwiwa, Malam Sale Ahmed Zauma ya ce sun ziyarci Mai Martaba Sarkin ne domin kai masa ziyarar ban girma a matsayinsa na uban ƙasa da kuma neman shawarwarinsa.
Ya ce ƙaramar hukumarsa ta gudanar da muhimman ayyukan raya ƙasa da suka haɗa da gina hanyar motar birji mai tsawon kilomita tara da ta tashi daga Gwiwa zuwa Tinkishi zuwa Daurawa.
Kazalika, ya ce sun kuma samar da ruwan sha da inganta harkokin kiwon lafiya da ilimi da kuma bunƙasa tattalin arziki.
Daga nan ya yi kira ga jama’ar yankin da su ci gaba da bada haɗin kai da goyan baya domin cimma kyawawan manufofin da aka sanya a gaba.