Mun shirya zaɓen Anambra ba gudu ba ja da baya – INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu ya bayyana cewa INEC ta shirya tsaf domin gudanar da sahihin zaɓe a ranar 6 ga Nuwamba, 2021 a Jihar Anambra.

A ranar 6 ga wata ne za a yi zaɓen gwamnan jihar, a yayin da ake cikin zaman ɗarɗar a jihohin Kudu maso Gabas, musamman a Anambra, inda tsagerun ƙungiyar IPOB su ka yi barazanar hana gudanar da zaɓen.

Sun ce ba za su bari a yi zaɓe ba har sai gwamnatin tarayya ta sako masu gogarman su, Nnamdi Kanu wanda ke tsare a hannun jami’an SSS.

Sai dai kuma Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta bayyana shirin tura zaratan ta sama da dubu 30 domin tabbatar da an kiyaye doka da oda.

Ita kuwa Hukumar Tsaro ta Fararen Kaya (SSS), cewa ta yi kada tsagerun IPOB su kuskura su nemi tayar da zaune-tsaye a ranar zaɓen.

Yayin da ya ke jawabi a gaban Gamayyar Kwamitin INEC da Harkokin Zaɓe, na Majalisar Dattawa da na Tarayya, Shugaban INEC Yakubu ya ce INEC a shirye ta ke.

“Kwanan nan mu ka murmure daga hare-haren da aka riƙa kai wa ma’aikatan mu a wurare daban-daban. Kuma an kai hare-haren kan kayayyakin INEC.

“Amma dai mu na farin cikin cewa tuni mun tura dukkan kayan aikin zaɓe waɗanda ba masu hatsarin bari a fili ba ne.

“Za mu iya bugun ƙirji mu ce mun shirya wa zaɓen gwamnan jihar Anambra. Saboda mun samu ganawa da shugabannin direbobin motocin sufuri a ƙarƙashin NURTW, domin su ne za su yi aikin jigilar raba kayan zaɓe.” Inji Yakubu.