‘Yan bindiga sun yi garkuwa da farfesa da ‘ya’yan sa a Jami’ar Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA da MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Wata majiya ta shaida wa Manhaja cewa tun ƙarfe ɗaya na daren Talata ne wasu ‘yan bindiga suka dira jami’ar Abuja inda suka sace wani farfesa da ‘ya’yan sa biyu.

Farfesan mai suna Obansa Joseph yana karantarwa ne a sashen koyar da Tsimi da Tattali wato Economics a jami’ar.

Bayan shi da suka sace sun yi awon gaba da ‘ya’yan sa biyu wanda ba a bayyana sunayen su ba.

Haka kuma mahukuntan jami’ar sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun sace wasu ma’aikatan jami’ar su shida waxanda ba malamai ba ne, duk sun yi awon gaba da su.

Jami’in Hulɗa da Jam’a na jami’ar, Habib Yakoob, ya bayyana cewa tuni an sanar da jami’an tsaro kuma sun fantsama farautar ‘yan bindigan.

A yayin harin da aka kai da sanyin safiyar yau Talata, maharan sun yi awon gaba da mutane bakwai, waɗanda suka haɗa da wasu ma’aikatan cibiyar da iyalansu.

Shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU), reshen UNIABUJA, Dakta Kassim Umaru, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Waɗanda aka sace ɗin sun haɗa da Farfesa Obansa da ɗansa; Farfesa Oboscolo shi ma da ɗansa da ‘ya’yansa mata, sai kuma Sambo Mohammed da kuma Dakta Tobins.

“Don Allah muna buƙatar addu’o’in ku don dawowar su lafiya,” inji shugaban ASUU a cikin wani saƙo.

An ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na asuba a rukunin gidajen manyan ma’aikata da ke Giri a ƙaramar hukumar Gwagwalada a babban birnin ƙasar.