Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Fitaccen manazarci kan harkar siyasa, Farfesa Abubakar Ahmad Abdullahi ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira annobar siyasa da ka iya afkawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Jihar Zamfara, yana mai gargaɗin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Sanata Abdulaziz Yari da Gwamna Dauda Lawal na iya rasa Zamfara a babban zaɓen 2027.
Farfesa Abdullahi ya fitar da wannan sanarwa ga manema labarai a Gusau a yau Litinin, biyo bayan ficewar wasu ƴan majalisar dokokin Jihar Zamfara su takwas masu ci daga jam’iyyar APC.
A cewarsa, ƴan majalisar a wasiƙu daban-daban da suka rubuta wa shugabannin mazaɓunsu sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar ta APC yana mai cewar ta hanyarta suka yi ƙarfin adawa ga Gwamna Dauda Lawal a lokacin yana PDP.
Manazarcin ya bayyana ficewar ‘yan majalisar babban abin kunya ne ga shugabannin siyasa na jihar, musamman darakta-janar na kwamitin yaƙin nema zaɓen Tinubu/Shettima, Sanata Abdulaziz Yari, da kuma nuna alamar cewa akwai rikicin cikin gida a jam’iyyar ta APC.
“Jam’iyyar da a yanzu take cewa za ta samu ƙuri’u masu yawa ga Shugaba Tinubu da Gwamna Dauda Lawal a 2027 tana zaune ne a kan ganga mai ɗauke da bama bamai,” in ji shi.
Farfesa Abdullahi ya ɗora alhakin mafi yawan matsalolin siyasa a jihar a kan Gwamna Dauda Lawal, yana cewa bisa ga ofishinsa, shi ne shugaba da ke da cikakken ikon zartarwa.
A cewarsa, tun daga lokacin da rikici ya ɓarke a majalisar dokokin Jihar, gwamna Dauda Lawal ya kamata ya yi kira da a kwantar da hankali da fahimta amma maimakon haka ya ƙara rura wutar rikicin don amfanin kansa.
Yana mai nuna damuwar sa bisa yadda aka yi watsi da mambobin majilasar su takeas gaba ɗaya kuma an hana su duk wata hanyar yin sulhu da haƙƙoƙin su.
“Abin da ake tsammani shi ne, lokacin da gwamnan ya fice daga PDP zuwa APC a farkon wannan shekara, za a magance rikice-rikicen da ke cikin majalisar, amma babu ɗaya daga cikin shugabannin da ya damu,” in ji shi.
Manazarcin siyasar ya kuma caccaki Sanata Abdulaziz Yari, yana cewa jama’a na iya rashin jin daɗin yadda Yari ke yawo kamar wani ƙaramin ubangiji a matsayin DG na PCC kuma suna jiran lokaci daidai don su saka shi a inda ya dace.
“Akwai sansanonin da ke wanzuwa a ɓangaren Yari da kuma ɓangaren Matawalle na rashin jituwa kuma abun la’akari ne, to babbar damuwar shi ne matsalar za tana iya haifar da rashin samun nasarar shugaban ƙasa Tinubu a 2027.”
Farfesa Abdullahi ya ce abin ya fi tsanani a yankin Zamfara ta Yamma na Sanata Yari, inda biyar daga cikin masu ficewar takwas suka fito, wanda ya shafi ƙananan hukumomi biyar daga cikin shida a yankin.
A cewarsa, ficewar Hon. Aliyu Ango Kagara, mai wakiltar Talata Mafara ta Kudu – ƙaramar hukumar Yari kanta, wanda aka fi sani a matsayin mai biyayya ga Yari kuma wanda tasirinsa ya watsu a kan sauran mambobin da suka fusata wata babbar matsala ce ga nasarar APC a Jihar.
Sanarwar ta tuna cewa an dakatar da ƴan majalisar ne a ranar 27 ga Fabrairu, 2024, daga shugabancin Bilyaminu Moriki bisa zargin keta Dokar Aiki ta 10, Ka’ida ta 9 ta Majalisar, amma mambobin sun dage cewa an hukunta su ne saboda sun nuna damuwar su. kan ƙaruwar rashin tsaro a mazaɓunsu.
Ya ce tsawon watanni 31 sun kasance a dakace ba tare da albashi ko alawus ba wanda ya saɓa wa ƙa’idojin majalisa.
Farfesa Abdullahi ya bayyana ƙalubalen a matsayin rarrabuwar kawuna mai zurfi tsakanin ɓangaren Matawalle dana Sanata Yari, inda majiyoyi ke cewa Sanata Abdulaziz Yari baya goyon bayan Gwamna Dauda Lawal, yayin da tsofaffin ƴan jam’iyyarsa ke sake haɗuwa don tsara yadda za su kaɗa masa ƙuri’a.
Ya kuma lura cewa masana da yawa sun yi imanin cewa manufofin Gwamnan suna da tsauri, musamman ƙwazo na tara kuɗaɗen shiga, haraji mai yawa, da korar ƴan ƙasa da yawa da yanzu ba su da aikin yi.
“Akwai buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani ta hanyar gayyatar manyan ƴan siyasa uku, Matawalle, Yari da Gwamna Dauda Lawal zuwa teburin tattaunawa kan yadda za a sake tsara jam’iyyar APC ta Zamfara don samun nasara,” in ji shi.
