Al-Makura ya bayyana goyon bayansa ga tsohon Sufeto Janar Adamu gabanin zaɓen fidda gwani na APC a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN WADA a Lafia

Umaru Tanko Al-Makura tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma mai kula da yankin Arewa ta tsakiya na ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors ya bayyana goyon bayansa a fili ga neman tikitin gwamna na tsohon sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammed Abubakar Adamu.

Sanarwar ta fito ne a ranar Lahadi a fadar mai martaba sarkin Lafia Mai Sheri’a Sidi Bagel inda Al-Makuran wanda shi ne kuma shugaban hukumar ilimi ta ƙasa na matakin farko yayi jawabi a ƙarshe na yawon shawara da Adamu yayi wa fadar sarakunan gargajiya a faɗin jihar.

Al-Makura ya bayyana cewa dalilin da yasa ya yanke shawarar haka shi ne ganin halayen shugabanci na Adamu waɗanda yake ganin sun sa ya zama ɗan takara da yafi dacewa ya jagoranci jihar ta Nasarawa zuwa saurin cigaba. Ya ce gudanar da taron rufe yawon a fadar Lafia abu ne da ya dace domin garin Adamu ne kuma wurin danginsa.

“Wannan ba ziyarar girmamawa ba ce kawai ba, aikin ɗan gida ne ya koma gida bayan ya gana da shugabanni da sarakuna a faɗin jihar,” in ji Al-Makura. “Da zaɓen fidda gwanin gwamna na APC ya rage kwanaki uku kacal, wannan lokaci ne na ba mahaifinsa labarin ci gaban da aka samu da neman albarka, shawara, da goyon baya. A yau mun tsaya a gabanka da magoya bayan Adamu domin miƙa girmamawa ta musamman, wadda ta sha bambam da waɗanda aka miƙa a sauran fada.”

Ya nuna yaƙinin cewa Adamu zai yi nasara a zaɓen fidda gwanin dake tafe yana mai jaddada cewa tsohon Sufeto Janar ɗin yana da ƙarfin kai Nasarawa zuwa wani mataki mafi girma. Al-Makura ya kuma jaddada cewa tsarin ya zama na dimokuraɗiyya, ba tare da amincewa ko yarjejeniya ba, domin kada ƙuri’a jama’a ta zama mara amfani.

“Muna da yaƙinin za ka yi alfahari da IGP Adamu da tawagarsa,” ya gaya wa Sarki. “Za mu bi doka da ƙa’idoji mafi kyau. Da izinin Allah, za mu fito da nasara.”

Al-Makura ya ƙara maraba da shawarar shugaba Bola Tinubu da shugabancin APC na amfani da zaɓen fidda gwanin kai tsaye a Nasarawa yana mai cewa hakan ya mayar da iko hannun jama’a kuma ya sa amincewar mutum ɗaya babu amfani.

Shi kuwa Adamu a nasa ɓangaren ya gode wa Sarkin Lafia Mai Shari’a Sidi Bage (mai ritaya) bisa karɓar shi da tawagarsa. Yace ya zo ne da farko domin neman albarka da addu’a kafin ya fara yaƙin neman zaɓensa kuma zai cigaba da sanar da sarkin shirinsa.

“Na nemi albarkarka da addu’arka da jagorancin ka,” in ji Adamu. “Ka ba mu shawara mu guji ruɗani ka kuma tabbatar mana cewa masarauta da mutanen Lafia suna bayanmu. Ka ce mu nemi goyon baya a wasu wurare kuma da goyon bayan jama’a za mu yi nasara. Mun bi wannan shawara muka zagaya faɗin jihar muka samu karɓuwa sosai.”

Adamu ya yarda cewa rarrabuwar kawuna ta taso a cikin jam’iyyar saboda sha’anin waje, amma ya ce ya ci gaba da mai da hankali kan burinsa. Ya yi alƙawarin gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana bisa ƙa’idojin INEC.

A martaninsa, sarki yayi wa tawagar Adamu fatan alheri a gasar inda ya kuma buƙace su da su riƙo zaman lafiya da ladabi komai sakamakon zaɓen fidda gwanin

By ukarofi