Daga JOHN D. WADA a Lafia
Ɗan takarar kujerar sanatan Arewacin jihar Nasarawa a zaɓen fidda gwanin dake tafe ƙarƙashin jam’iyyar Nijeriya Democratic Congress [NDC] Arch. Duba Ishaya-Dodo yayi alƙawarin ƙarfafa tare da tallafa wa mata da matasa da bunƙasar ababen more rayuwa fifiko.
Arch. Ishaya-Dodo ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Lafia fadar gwamnatin jihar.
A cewarsa dalilin da yasa ya shiga takarar kujerar sanatan Arewacin Nasarawa shi ne saboda yana da sha’awar yi wa mutanen yankin hidima.
Ishaya-Dodo ya ce yana da ƙarfin gwiwa da ƙwarewar da za ta ba shi damar wakiltar mutanen mazaɓar Arewacin Nasarawa yadda ya kamata.
Ya ƙara da cewa ganin muhimmancin yankin zai kawo sabbin dabaru da za su hanzarta cigaban mazaɓar sanatan baki ɗaya.
Ya cigaba da bayyana cewa “Zan kawo abubuwa da yawa a kan tebur nawa duka hidima ne zanyi wa al’umma ta tabbas da wakilci nagari tare da ƙarfafa gwiwar mata da matasa gaba ɗaya kamar dai aƙidar NDC na yin hidima ga jama’a ba wai muna waƙa ne kawai ba,” in ji shi.
Ishaya-Dodo yayin da yake roƙon masu kaɗa ƙuri’a da su buɗe zuciyarsu ga sabbin dabaru ya kuma ce NDC ita ce kawai jam’iyyar da ke da ƙarfin ceto Najeriya daga nutsewa.
“Saboda haka ina shawartar kowane mai kaɗa ƙuri’a da kada ya sayar da ƙuri’arsa kada su bi alƙawuran ƙarya na jam’iyyar da ke mulki.
“A yanzu Najeriya ba ta aiki kuma NDC ta zo ne domin gyara Najeriya. Saboda haka ina shawartar masu kaɗa ƙuri’a da su haɗa kai da NDC domin gyara Najeriya. Mu mayar da Najeriya zuwa zamanin da muke tunawa da jarumawan da suka gabace mu,” in ji shi.
